Gwamnonin jam’iyyar adawa ta PDP sun zargi Shugaban Kasa Muhammadu Buhari da mayar da Fadar Gwamnatin Najeriya a matsayin Hedkwatar Jam’iyyar APC.
A yayin taron da suka gudanar a Jihar Bauchi, gwamnonin sun ce Fadar Gwamnatin Najeriya wacce mallaki ce ga duk al’ummar kasar, a yanzu Buhari ya mayar da ita tamkar sabuwar Hedikwatar jam’iyyar APC.
- Karin dalibai 3 sun kubuta daga hannun ’yan bindiga a Kaduna
- Atletico ta nada Fernando Torres kocin matasa
A taron na ranar Litinin wanda suka tattauna kan halin da dimokuradiyyar Najeriya ke ciki da sauran batutuwa, sun kuma zargi Gwamnatin APC da amfani da wani salo na tursasa wasu gwamnonin PDP komawa jam’iyyar mai mulki.
Gwamnonin sun kuma yi zargin cewa gwamnatin jam’iyyar mai mulki ta lalata tattalin arzikin kasar, tare da mayar da Najeriya filin kashe-kashe da babu abin da ta tsinana face jefa al’ummar cikin kunci saboda rashin iya jagoranci.
“Muna Allah wadai da salo na rashin gaskiya da ake bi wajen tilasta wa gwamnonin PDP da sauran masu ruwa da tsaki don komawa APC, jam’iyyar da gurgunta tattalin arzikin kasar kuma ta mayar da kasar filin kashe-kashe da haifar da kunci a tsakanin al’umma.”
Gwamonin jam’iyyar adawar sun bayyana zarginsu karara kan cewa ba za su amince da tsarin ’yar tinke ba a zaben fidda gwani da gwamnatin ke kokarin tilasta wa jam’iyyu aiwatarwa a cikin kudin yi wa dokar zabe kwaskwarima da ke gaban Majalisa.
A cewarsu, “wannan tsarin na ‘yar tinke zai bayar da damar tafka magudi kamar yadda Shugaba Buhari ya samu kuri’a miliyan 15 a zaben fitar da gwani na APC a 2018 amma ya samu miliyan 15 kacal a babban zabe na 2019.”
Sun bayar da shawarar cewa a kyale jam’iyyu su yanke hukunci kan gudanar da zaben ’yar tinke ko sabanin haka.
Kazalika, zauren gwamnonin ya umarci dukkan ’yan Najeriya da su samar wa da kansu makamin siyasa domin ceto Najeriya.
“Muna kira ga dukkan ’yan kasa na gari da su yi amfani da wannan dama ta rajistar zabe da ake gudanarwa ta yadda za su samu makamin ceto kasar daga gwamnatin APC.”