Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya sauka a Jihar Filato domin gudanar da ziyarar aiki na kwana biyu.
Jirgin Shugaban ya sauka ne a filin jirgin Heipang da misalin karfe 11 da minti 54, sannan kuma ya samu tarba daga Gwamnan Jihar Simon Lalong da tsofaffin gwamnonin jihar, Sanata Joshua Dariye da Jonah Jang da minsitan Harkokin wasanni da al’adu Solomon Dalung da tsohuwar mataimakiyar gwamnan jihar Dame Pauline Tallen da sauransu