✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Buhari ya jinjina wa gwamnatin Adamawa wajen yaki da cin hanci da rashawa

Shugaba Muhammadu Buhari ya jinjinawa gwamnatin Jahar Adamawa domin bin sawunsa wajen yaki da rashawa da cin hanci da kuma almundahana. Ya ce ba zai…

Shugaba Muhammadu Buhari ya jinjinawa gwamnatin Jahar Adamawa domin bin sawunsa wajen yaki da rashawa da cin hanci da kuma almundahana. Ya ce ba zai fasa ba wajen yaki da rashawa da cin hanci har sai ya ga karshensa a kasar ta kare baki daya.

Ya bayyana hakan ne jiya a lokacin da ya kai ziyara Jahar Adamawa domin bude wani taro akan yaki da rashawa da cin hanci da kuma almundahana wadda aka yi a gidan gwamnatin Jihar Adamawa.

Ya nuna matukar farin cikinsa domin ganin yadda gwamnatin Jahar Adamawa ta biyo sawunsa kuma ya ce ya gamsu da irin yadda gwamnan jahar, Muhammad Bindow ke tafiyar da harkar jahar wajen yaki da rashawa.

Ya kuma kara da cewa babu abin da yake kawo cigaba fiye da hadin kai da bin doka da kuma yadda ‘yan majalisar jiha da kuma gwamnatin jiha hade da kananan hukumai suke bin na gabansu sau da kafa, domin ci gaba da samun nasara a jahar baki daya.

Sannan sai ya kirayi sauran gwamnonin jihohi da su yi koyi da Bindow da kuma al’umman jahar Adamawa wajen ba shi goyon baya dari bisa dari. 

Sakataren Gwamnatin Jahar Adamawa, Dakta Umar Bindir wadda ya yi jawabi akan ayyukan da Gwamnatin Bindow ta aiwatar, ya nuna yadda gwamnatin ta canja al’amura cikin kankanin lokaci.

Bindir ya ce gwamnatinsu ta kammala kwangiloli 90 wadda aka rubutu a tsarin kasafin kudi na shekarar 2017 sannan gwamnatin ta ninka kudade daga miliyan 150 zuwa miliyan 700 har zuwa miliyan 850.

A fadar Lamidon Adamawa, inda Shugaba Muhammadu Buhari ya fara ziyarta, Lamidon na Adamawa, Alhaji Aliyu Mustapha Barkindo ya bukaci Shugaban da ya taimaka wajen mayar da jami’ar Modibbo Adama zuwa tsararriyar jami’a wadda za a iya karanta kowane fanni na karatu ba lallai bangaren kere-kere da kimiyya kadai ba, sannan ya sake neman shugaban kasar da ya mayar da asibitin gwamnatin FMC zuwa asibitin koyarwa a jahar.