Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya jagoranci zaman Majalisar Zartarwa da aka saba gudanarwa duk mako a fadarsa ta Aso Villa da ke birnin Abuja.
Taron wanda ya fara gudana da safiyar Laraba ya samu halarcin Mataimakin Shugaban Kasa, Farfesa Yemi Osinbajo da Sakataren Gwamnatin Tarayya, Boss Mustapha da Shugaban Ma’aikatan Fadar Shugaban Kasa, Farfesa Ibrahim Gambari da Mai Ba da Shawara kan Harkokin Tsaro na Kasa, Babagana Monguno.
Ministoci takwas ne kacal suka halarci taron a babban dakin taro na Council Chambers yayin da ragowarsu da kuma Shugabar Ma’aikatan Gwamnatin Tarayya, Folasade Yemi-Esan suka halarta daga nesa ta hanyar bidiyo.
Daga cikin ministocin da suka hallara a wurin taron akwai Rotimi Amaechi na Ma’aikatar Sufuri; Ministan Harkokin Cikin Gida, Rauf Aregbesola; da Ministar Kudi, Kasafi, da Tsare- Tsare, Zainab Ahmed.
Sauran sun hadar da Ministan Shari’a, Abubakar Malami; Ministan Harkokin Neja Delta, Godswill Akpabio; Ministan Ayyuka da Gidaje, Babatunde Fasola; Ministan Labarai da Al’adu, Lai Mohammed; da kuma Minista a Ma’aikatar Albarkatun Mai, Timipre Sylva.