✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

NAJERIYA A YAU: Tasirin Dangantakar Bangaren Zartarwa Da Na Majalisa A Kan Talaka

Shin yaya ya kamata dangantaka ta kasance a tsakanin bangaren zartarwa da majalisar dokoki a tsarin mulkin dimokuraɗiyya?

More Podcasts

A tsarin mulkin dimokuraɗiyya, dangantaka tsakanin bangaren zartarwa da majalisun dokoki tana taka muhimmiyar rawa wajen gudanar da shugabanci a tsakanin al’umma.

A galibin kasashe masu bin tsarin na dimokuraɗiyya, ’yan majalisa kan kasance masu wakiltar al’umma da kare muradunta, da sa ido da kuma bayar da shawarwarin da suka dace ga bangaren zartarwa domin ci-gaban kasa.

Sai dai a Najeriya, a wasu lokutan akan zargi ’yan majalisa da zama ’yan-amshin-Shata.

Ko me ya sa haka? Shin yaya ya kamata dangantaka ta kasance a tsakanin bangaren zartarwa da majalisar dokoki a tsarin mulkin dimokuraɗiyya?

Wannan shi ne batun da shirin Najeriya A Yau na wannan lokaci zai duba.

Domin sauke shirin, latsa nan