Gwamnan Jihar Borno, Babagana Zulum, ya karbi bakuncin Shugaban Kasa Muhmmadu Buhari domin kaddamar da manayn ayyukan da gwamnan ya kammala a Maiduguri, fadar jihar.
A rnaar Alhamis ne Buhari ya isa Maiduguri domin kaddamar da ayyukan da suka hada da gidajen malamai da wasu gidaje 500 da gwamnan ya gidan wa ’yan gudun hijira da suka rasa muhallansu.
- Kamfanin Emirates ya dakatar da aiki a Najeriya kan rikicin kudi
- Sata a kotun Musulunci: Kotu ta tsare ‘barawo’ a gidan yari
Tagawar Zulum da ta tarbi Buhari ta had da mataimakin gwamnan Usman Kadafur, Ministarn Kyautata Rayuwa Sadiya Umaru Farouk, dan takarar mataimakin shugaban kasa a Jam’iyyar APC, Sanata Kashim Shettima, ’yan Majalisar Dokokin Jihar Borno da manyan jami’an gwamnaitn jihar.