Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya gayyaci Ministan Lantarki, Abubakar Aliyu don tattauna yadda za a shawo kan matsalar karancin wutar lantarki da ake fama da ita a fadin Najeriya.
Kazalika, shugaba Buhari ya gayyaci gwamnan Jihar Imo, Hope Uzodinma da mai ba shi shawara kan harkokin tattalin arziki, Farfesa Doyin Salami, don tattaunawa kan sha’anin tsaro a Kudancin kasar nan da kuma abin da ya shafi tattalin arziki.
- Ba na takarar kowace kujerar siyasa – Shugaban ITF
- Abin da muke so a yi muddin ana son kawo karshen ta’addanci – Turji
Hadimin shugaban kasa, Garba Shehu ne ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da ya fitar, inda ya ce Buhari zai gana da su da yammacin ranar Litinin a Fadar Villa da ke Abuja.
Shehu ya bayyana yadda shugaba Buhari ya yi Allah wadai da harin da wasu bata-gari suka kai kan ofishin ‘yan sanda a Jihar Imo.
Buhari ya shaida cewa dole ne a sake yin shiri na musamman kan yadda ake ci gaba da samun hare-hare a wasu sassan kudancin kasar nan.
Idan ba a manta ba a satin da ya gabata ne shugaba Buhari ya nemi afuwar ‘yan Najeriya kan yadda karancin wutar lantarki ke ci gaba da ta’azzara.