✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Buhari ya gana da Tinubu a Aso Rock

Ana tsammanin Buhari da Tinubu sun tattauna halin da ake ciki game da matsalar canjin kudi.

Shugaba Muhammadu Buhari ya yi wata ganawar sirri da dan takarar Shugaban Kasa na jam’iyyar APC, Asiwaju Bola Tinubu a Fadar Gwamnatin Tarayya.

Wata sahihiyar majiya ta ce an gudanar da taron ne a sirrance gabanin taron Majalisar Zartarwa da Buharin ya jagoranta a ranar Laraba.

Aminiya ta gano cewar ganawar ba za ta raba nasaba da batun yakin zabe da kuma sauran matsalolin da kasar nan ke fuskanta ciki har da batun karancin takardun kudi.

Aminiya ta ruwaito cewar Shugaban Kasa ya halarci zaman majalisar a makare a karon farko da misalin karfe 10:40 na safiyar ranar Laraba.

Taron wanda aka fara minti 40 bayan lokacin da aka tsara, ya samu halartar Sakataren Gwamnatin Tarayya, Boss Mustapha da Shugabar Ma’aikatan Tarayya, Dokta Folasade Yemi-Esan.

Wata majiya ta ce shugaba Buhari, ya isa wajen taron a makare ne saboda yana sa ido kan zaman sauraron shari’ar da Kotun Koli ta yi dangane da kalubalantar matakin Babban Bankin Najeriya (CBN) na aiwatar da wa’adin amfani da tsoffin takardun kudi.

A halin yanzu dai Kotun Kolin ta dage shari’ar zuwa har ranar Laraba, 22 ga watan Fabrairu.

Gwamnonin jihohi 10 na kalubalantar manufar musayar tsofaffin takardun kudi a Kotun Koli.

Kotun Kolin ta ce har yanzu umarnin da ta bayar na dakatar da aiwatar da wa’adin ranar 10 ga watan Fabrairu kan tsofaffin kudi na nan daram.

Sauran wadanda suka halarci zaman Majalisar Zartarwa sun hada da Ministan Yada Labarai da Al’adu, Lai Mohammed, Ministan Shari’a, Abubakar Malami (SAN), Ministan Sadarwa da Tattalin Arzikin Zamani, Isa Ali Pantami, Ministar Kasafin Kudi da Tsare-tsare ta Kasa, Zainab Ahmed.

Sauran sun hadar da Ministan Birnin Tarayya, Mohammed Bello da Ministan Ilimi, Adamu Adamu.

Akwai kuma Ministan Lafiya, Dokta Osagie Ehanire, Ministar Bayar da Agaji da Jin Kan Jama’a, Sadiya Farouq da kuma Karamin Ministan Noma, Mustapha Shehuri da sauransu.