✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Buhari ya gana da sabuwar Shubagar WTO, Okonjo-Iweala

Shugaba Buhari ya yi ganawar sirri da sabuwar shugabar Kungiyar Kasuwanci ta Duniya (WTO), Ngozi Okonjo-Iweala, a Abuja.

Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya yi ganawar sirri da sabuwar Shugabar Kungiyar Kasuwanci ta Duniya (WTO), Ngozi Okonjo-Iweala, a Fadar Fwamnatin Tarayya da ke Abuja.

Sabuwar Darakta-Janar din ta WTO kuma tsohuwar Ministar Kudi da Tattalin Arziki a Najeriya, ta samu tarba daga Shugaban Ma’aikatan Fadar Shugaban Kasa, Farfesa Ibrahim Gambari, a ranar Litinin.

Okonjo-Iweala ta samu rakiyar Ministocin Masana’antu, Kasuwanci da Saka Jari, Niyi Adebayo; Harkokin Kasashen Waje, Geoffery Onyeama da Ministan Masana’antu, Kasuwanci da Zuba Jari, Maryam Katagum.

Har wa yau, a cikin wakilan da suka mata rakiya, akwai wasu jami’an WTO.

Tsohuwar ministar ta iso Najeriya ne a ranar Asabar, domin ziyarar aiki kwana biyar, bayan karbar ragamar shugabancin WTO a ranar 1 ga watan Maris, 2021.

Ana sa ran Okonjo-Iweala, za ta yi wa ’yan jarida bayani game da ganawarta da Shugaba Buhari, sannan ta yi wa Gwamnatin Tarayya godiya bisa gudunmawar da aka ba ta wajen samun kujerarta ta WTO.