A ranar Talata ne tsohon Shugaban Kasa Goodluck Jonathan ya gana da Shugaba Muhammadu Buhari, inda ya bayyana masa halin da kasar Gambiya ke ciki dangane da rikicin siyasar da ya dabaibayeta.
Bayan ganawarsa da Buhari, Jonathan ya shaida wa manema labari cewar ya ba wa Shugaban Kasar rahoton abin da aka tura shi yi a Banjul, babban birnin kasar Gambiya.
- Jonathan jajirtaccen mutum ne, inji Buhari
- Jonathan ya kai wa Buhari ziyarar godiya
- Hotuna: Jonathan ya ziyarci Buhari a fadar shugaban kasa
Jonathan wanda ya jagoranci tawagar ECOWAS lokacin kwantar da rikicin kasar Mali, ya ce an aika sa Gambiya ne domin nemo mafita game da rikicin siyasar da ya kunno kai a kasar.
Ya kara da cewa ya yi nasarar cimma kuduri na farko, yana kuma sa rran zai cimma kuduri na biyu daga nan zuwa Janairun 2021.
Shugaba kasar Gambiya Adama Barrow na da bukatar zarcewa a zaben da za a sake yi, wanda hakan ya haifar da hargitsi a kasar.
A ranar 3 ga watan Disamban 2020, Barrow ya gana da Shugaba Buhari a Abuja, inda ya nemi gwamnatin Najeriya ta agaza wa kasarsa.
Barrow ya shaida wa Buhari cewa kasarsa na neman taimakon Najeriya kamar yadda ta saba duba da kyakkyawar dangartakar da ke tsakaninsu.
Sai dai wasu daga cikin ‘yan adawa a kasar ta Gambiya sun bukaci shugaban kasar da ya sauka kamar yadda ya yi alkawarin yin zango daya a karagar mulki.
Shugaba Buhari a yayin ganawarsa da Barrow a ranar 3 ga Disamba 2020, ya shaida masa cewa ya jagoranci tawagar ECOWAS a 2016 domin sulhunta rikicin siyasa a lokacin Yahya Jammeh, amma duk da haka Buhari ya yi alkawarin taimaka wa kasar ta Gambiya.