✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Buhari ya gana da Jonathan a Aso Rock

Sai dai babu cikakkun bayanai kan ganawar tasu.

Shugaban Kasa Muhammadu Buhari, a ranar Alhamis ya gana da tsohon Shugaban Kasa, Goodluck Jonathan a fadar Aso Rock da ke Abuja.

Jonathan dai, wanda ya isa fadar da misalin karfe 3:00 na yamma, ya sami tarba daga Buharin, inda suka yi wata ganawar sirri.

Ko da yake babu cikakkun bayanai kan abubuwan da suka tattauna, amma ana kyautata zaton ba zai rasa nasaba da batun tura Jonathan din a matsayin jakadan kungiyar ECOWAS ba, inda yake shiga tsakanin rikicin siyasar kasar Mali.

Mali dai ta fada rikici ne tun bayan juyin mulkin da sojoji suka yi wa Shugaba Ibrahim Boubacar Keita a watan Agustan bara.

To sai dai a ranar Litinin, gwamnatin kasar ta Mali wacce sojoji suka fi yawa a cikinta ta kaddamar da wani taro na tsawon kwana hudu wanda zai yi shirye-shiryen mayar da kasar zuwa tafarkin Dimokradiyya.

Taron dai, a cewar Shugaban rikon kwaryar kasar, Kanal Assimi Goita, zai yi muhimmin nazari kan halin da kasar ke ciki da makomarta a nan gaba.

Sai dai ko kafin nan, Jonathan ya kasance jakadan na ECOWAS a kasar Gambia makonni uku da suka shude, don sasanta wani rikici da ke da alaka da zaben Shugaban Kasar na hudu ga watan Disamban 2021.