✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Buhari ya dawo daga Kenya, ya fasa zuwa Landan ganin likita

Da farko dai an tsara Buhari zai wuce Landan ne daga Nairobin.

Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya yi mi’ara koma baya inda ya dawo Abuja a daga kasar Kenya, a maimakon wucewa birnin Landan don ganawa da likitocinsa kamar yadda aka tsara tun da farko.

Hadimin Shugaban kan Kafafen Sadarwa na Zamani, Bashir Ahmad ne ya tabbatar da dawowar Shugaban ranar Juma’a, lamarin da ya sa mutane suke ta cece-kuce.

Buhari dai ya halarci wani taro ne a birnin Nairobi na kasar Kenya kan cika shekara 50 da kafa Shirin Muhalli na Majalisar Dinkin Duniya (UNEP), inda daga can ne aka tsara zai wuce Landan din don ganin likitocinsa.

A farkon makon nan ne dai Hadimin Shugaban Kasa kan Yada Labarai, Femi Adesina ya sanar da cewa Buharin zai wuce Landan don ganawa da likitocinsa daga Kenya.

“Daga kasar Kenya, Buhari zai wuce Landan don ganawa da likitocinsa na tsawon mako biyu,” inji Adesina a cikin sanarwar.

Sai dai a ranar Juma’a, Bashir Ahmad ya tabbatar da cewa Shugaban ya dawo Abuja.

“Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya dawo Abuja bayan ya halarci taron bikin cikar Shirin Muhalli na Majalisar Dinkin Duniya (UNEP) shekara 50a Kenya.

Sai dai mutane da dama sun fara nuna kokwantonsu tare da neman karin bayani kan musabbabin sauya shawarar.

Aminiya ta gano cewa Buhari ya sauka ne a filin jirgin sama na Nnamdi Azikiwe da ke Abuja da misalin karfe 1:00 na rana.

Sai dai har zuwa lokacin hada wannan rahoton, babu wata sanarwa a hukumance kan makasudin sauya shawarar.

Wannan dai ba shi ne karo na farko da Buharin yake soke tafiyar ganin likitan da ya tsara yi ba, inda ko a watan Yunin bara, sai da aka soke tafiyar, ’yan sa’o’i kafin lokacin da aka tsara yinta ba.