Gwamnatin Tarayya da na jihohi na shirin bullo da shirin noma domin mazauna birane mai suna Shirin Ciyar da Kanka, wato ‘Operation Feed Yourself’ a turance.
Mataimakin Shugaban Kasa, Yemi Osinbajo, ya ce manufar shirin ‘Operation Feed Yourself’ ita ce ba wa ’yan Najeriya mazauna birane kwarin gwiwar yin kananan gonaki da kuma lambuna a gidajensu domin ciyar da kansu.
- Daga Laraba: Illolin da bilicin ke haifar wa lafiyar masu yi
- Najeriya A Yau: Dalilan da ke jawo hauhawar farashin kayan masarufi
“Wannan zai taimaka wa daidaikun mutane, sannan za su iya sayar da rarar da suka samu daga abin da suka noma, wanda hakan zai taimaka wajen samar da wadataccen abinci a cikin kasa.
“Kafa gidajen gona ko cibiyoyin noma da gandun noma da saurasu zai taimaka wajen samar da lafiyayyen abinci; don haka muke ba da shawara a yi koyi da abin da Jihar Oyo ta yi ko makamancinsa da wata jiha za ta yi domin samun nasara a wannan bangare,” inji shi.
Osinbajo, wanda ya ce shirin zai kasance ne karkashin kulawar Majalisar Tattalin Arziki ta kasa, ya bayyana haka ne a babban taron samar da lafiyayyen abinci, wanda Mataimakiyar Sakatare-Janar ta Majalisar Dinkin Duniya, Amina Mohammed, ta halarta, tare da kungiyoyin jinkai na Dangote da Bill&Melinda Gates da gwamnoni da wakilan kungiyoyin ci gaban kasashe.
Ya ce “Gwamnatocin jihohi da tarayya za su tallata shirin na ‘Operation Feed Yourself’, wanda zai kunshi kafa gonakin zamani a birane da kuma lambuna a cikin gidaje.
“Wannan abu ne da ya kamata jama’a su runguma a fadin kasar nan, gwamnati kuma za ta taimaka ta hanyoyi daban-daban wajen ganin daidaikun mutane da makarantu sun mallaki lambuna na kashin kansu.”
‘Operation Feed Yourself’ daya ne daga cikin shirye-shirye uku da Najeriya ke shirin bullo da su bayan taron samar da ingantaccen abincin da ke da goyon bayan Majalisar Dinkin Duniya da nufin samar da lafiyayyen abinci.
Sauran sun hada da taimaka wa manoma a fadin Najeriya ta hanyar samar musu da bayanan da suka dace kan yanayi da kasar shuka da za su taimaka musu wajen samun amfani mai yawa.
Na ukun shi ne ba da kwarin gwiwa ga hukumomin Gwamnatin Tarayya da gwamnatocin jihohi domin su rika sakin kudaden da aka ware a kasafin kudadensu domin gudanar da ayyukan da suka danganci samar da lafiyayyen abinci.
Akwai kuma hadin gwiwa da hukumomin Majalisar Dinkin Duniya da kungiyoyin cigaban kasashe wajen aiwatar da ayyukan bunkasa samar da lafiyayyena abinci.