Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya umarci rundunar sojin kasa ta Najeriya da ta kawo karshen ayyukan ‘yan bindiga.
Buhari ya bayar da umarnin ne ranar Asabar bayan wasu hare-hare da wasu ‘yan bindiga suka kai a Zamfara da Kaduna.
Ya kuma yi Allah-wadai da kashe-kashen da ‘yan bindigar suka yi a jihohin biyu a cikin wata sanarwa da mai magana da yawunsa, Malam Garba Shehu, ya fitar.
- Jarumin Kannywood Sani SK yana neman taimako
- Abduljabbar da malaman Kano: An tashi ba a cimma matsaya ba
Shugaban kasar ya bukaci kawo karshen hare-haren da ‘yan bindiga ke kaiwa musamman a yankunan karkara.
Da yake nuna damuwarsa a kan kisan gillar da ‘yan bindiga ke yi wa wadanda ba su ji ba, ba su gani ba, Buhari ya umarci kawo karshen zubar da jinin da suke yi cikin kankanin lokaci.
Kazalika ya ce sojoji na bukatar samun hadin kan al’ummar kasar nan don kawo karshen ‘yan bindiga da ‘yan ta’adda.
Shugaba Buhari ya kara da cewa sojoji da sauran jami’an tsaro na aiki tare don nemo sabbin hanyoyin dakile ‘yan bindiga kuma tuni kwalliya ta fara biyan kudin sabulu.
Buhari ya soki wasu ‘yan siyasa da ke maganganu kan sha’anin tsaro, yana ba su shawara da su mayar da hankali wajen hada hannu da nufin dakile matsalar tsaro da ta addabi Najeriya.