Majalisar Zartarwa ta Tarayya (FEC) ta ba da lamunin fitar da Dala biliyan 3.1 domin karasa aikin inganta harkokin gudanarwa a Hukumar Hana Fasakwauri ta Najeriya (NCS).
Ministar Kudi, Kasafi da Tsare-Tsare, Zainab Shamsuna Ahmed, ce ta bayyana hakan yayin zantawa da manema labarai bayan halartar zaman Majalisar Zartarwa da Shugaba Buhari ya jagoranta a fadarsa da Abuja.
Ta ce makasudin hakan shi ne mayar da dukkan harkokin gudanarwa na Hukumar Kwastam su koma amfani da fasahar zamani musamman bangaren sadarwa da tattara bayanai.
- Fadar Shugaban Kasa ta magantu kan kamuwar Sarki Abba da coronavirus
- Dalilin da ya sa jami’o’i masu zaman kansu ke neman a bude makarantu –ASUU
A cewarta, yarjejeniyar kwangilar aikin na tsawon shekara 20 kudadenta za su fito ne daga masu zuba jari da kudaden shiga da ake sa ran samu daga Hukumar wadanda sun tasar ma Dala biliyan 176.
Ministan Labarai da Al’adu, Lai Mohammed, a nasa jawabin, ya jaddada cewa babu ko sisin kobo da Gwamnatin Tarayya za ta fitar daga lalitarta wajen gudanar da aikin.