✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

‘Buhari ya ayyana ’yan bindiga a matsayin ’yan ta’adda kawai’

El-Rufai ya bukaci a dauki sabbin jami'an tsaro 1,000 daga kowace karamar hukuma.

Gwamnan Jihar Kaduna, Nasir El-Rufai, ya bukaci Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya ayyana ’yan bindiga a matsayin ’yan ta’adda, domin sojoji su kashe su babu kakkautawa.

El-Rufai wanda ya ce tun a shekarar 2017 ya aike wa  Shugaba Bubari da takardar neman hakan, ya yi kira da a samu daidaito tsakanin Gwamnatin Tarayya da jihohi 36 da ke fadin Najeriya su dauki matakin gaggawa na daukar matasa 1,000 daga kowace karamar hukuma aikin tsaro, domin yi wa tufkar hanci.

“Muna goyon bayan masu kiraye-kiraye cewa a ayyana ’yan bindiga a matsayin ’yan ta’adda, kuma tun a shekarar 2017 muka aike wa Gwamnatin Tarayya da bukatar hakan domin a ba wa sojojinmu damar kai musu hare-hare da karkashe su ba tare da tunanin karya wata doka ba.

“Muna goyon bayan wannan matsayi da Majalisar Dokoki ta dauka, sannan za mu bi sahun wasikar da muka tura domin ganin cewa Gwamnatin Tarayya ta ayyana wadannan ’yan bindigar a matsayin ’yan ta’adda domin sojoji su samu cikakkiyar damar kashe su ba tare da fargabar karya wata dokar kasa da kasa ba. Wannan shi ne matsayin Gwamnatin Jihar Kaduna,” a cewarsa.

Ya bayyana haka ne a ranar Laraba bayan ya karbi rahoton yanayin tsaron jihar na watan Yuli zuwa Satumba, 2021, daga Kwamishinan Tsaron Jihar, Samuel Aruwan.

A cewarsa, daukar jami’an tsaro 1,000 a kowacce daga kananan hukumomin kasar nan 774 zai tamaika wajen ragargaza ayyukan miyagu da sauran bata-gari a Najeriya.

Ya kuma mika ta’aziyyarsa ga iyalan jami’an tsaro da suka kwanta dama, yana mai bayyana damuwarsa game da irin barnar da masalar tsaro ke yi wa al’amuran rayuwar jama’a.