✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Buhari ya amince da bude kwalejojin fasaha a wasu jihohi uku

Za a bude kwalejojin ne a jihohin Abia, Delta da Kano.

Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya amince a bude karin sabbin kwalejojin fasaha na tarayya a wasu jihohi uku na Najeriya.

Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da ta fito ranar Talata ta hannun Daraktan Yada Labarai da Hulda da Al’umma na Ma’aikatar Ilimi ta Tarayya, Mr Ben Goong.

Mr Goong ya ce jihohin da za a bude makarantun sun hada da Kano da Abia da kuma Delta.

Sanarwar ta nuna Shugaba Buhari ya amince da wannan matakin ne a yunkirin samar da wadatattun makarantu a sassan kasar don amfanin talakawa.

A cewar Mr Goong, za a bude makarantun ne a Karamar Hukumar Umunnoechi ta Jihar Abia, da Karamar Hukumar Orogun a Jihar Delta, sai kuma Karamar Hukumar Kabo a Jihar Kano.

Ya kara da cewa, ana sa ran sabbin makarantun za su soma aiki a watan Oktoban 2022.

Ya ce bayan kammalawa, hakan zai rubanya adadin Kwalejojin Fasaha na Tarayya da ake da su a fadin kasar zuwa 36, ta yadda kowace jiha zai kasance tana da kwaleji daya.

Kano na da jami’o’i da manyan makarantu na gwamnatin Tarayya da gwamnatin jiha, abin da ya sa wasu ke cewa ba a bukatar karin wasu.