✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Buhari na sane da taron da na kira, inji Giadom

Mukaddashin shugaban jam’yyar APC na riko, Hilliard Eta ya ce tsohon Mataimakin Sakataren jam’iyyar da kotu ta dakatar, Victor Giadom ba shi da hurumin kiran…

Mukaddashin shugaban jam’yyar APC na riko, Hilliard Eta ya ce tsohon Mataimakin Sakataren jam’iyyar da kotu ta dakatar, Victor Giadom ba shi da hurumin kiran taron Kwamitin Zartawar jam’iyyar (NEC).

Giadom wanda ke da’awar shugabancin jam’iyyar  ya kira taron NEC da ya ce za a gudanar a ranar Alhamis at fasahar teleconference, kuma da sanin Shugaban Kasa Muhammadu Buhari za a yi.

Sanarwar tashi na zuwa ne a ranar da Babban Kotun Jiharsa ta Ribas ta dakatar da shi daga gabatar da kansa a matsayin dan jam’iyyar APC ko jami’inta.

‘Da sanin Shugaba Buhari za a yi’

Amma ya ce yana kiran taron ne dogaro da umarnin Kotun Daukaka Kara da a baya ta ba shi izinin zama shugaban riko bayan dakatar da Adams Oshiomhole daga kujerar.

“Bisa umarnin kotun da na samu na zama Mukaddashin Shugaban Jam’iyyarmu in kuma jagoranci tarukan Kwamitocin Gudanarwa na Kasa (NWC) da kuma NEC, kuma da izinin Shugaban Kasa Muhammadu Buhair (shugaban jam’iyya na kasa) ina kiran taron NEC da a baya aka shirya yi ranar 17 ga watan Maris 202o amma aka dage.

“Domin kiyaye ka’idojin kariya na COVID-19, za a yi taron ne ta intanet, inji sanarwar.

Sokiburutsu ne kawai, inji Eta

Sai dai a martaninsa, Prince Hilliard Eta, wanda ke rike da mukamin a madadin Sanata Abiola Ajimobi da uwar jam’iyyar ta nada shugaban riko ya ce taron da Giadom din ya kira haramtacce ne domin ba shi da hurumin yin hakan.

Da yake amsa tambayoyin ‘yan jarida, Eta ya ce, “Ni nan ina zama ne a madadin Sanata Abiola Ajimobi, shugaban jam’iyyarmu na riko.

“Idan har Giadom ya kira taron NEC, to hakkinku ne ku ‘yan jarida ku bincika ku ji ko shin yana da hurumin kiran taron.

“Yanzu haka kotu mai cikakken hurumi ta dakatar da Cif Giadom daga zama dan jam’iyya. Daga yau shi ba ma dan jam’iyya ba ne, balle har ya zama dan dan NWC.

Shi ya sa muke mamaki idan muka ji ana kiran shugaban bangare.

Sai dai ya musanta zargin da ake yi cewa uwar jam’iyyar na cikin rikici da ya mayar da ita tamfar fagen yaki.

A ranar Talata ce ‘yan sanda suka rufe ofishin jam’iyyar na kasa biyo bayan rikicin shugabancin da ya ki ci,  ya ki cinyewa a jam’iyyar, tun bayan dakatarwar da kotu ta yi wa shugaban jam’iyyar, Adams Oshiomhole.