✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Buhari na jagorantar taron Majalisar Zartarwa ta Kasa

Shugaban Kasa Muhammadu Buhari na jagorantar taron Majalisar Zartarwa ta Kasa na wannan mako ta bidiyo daga Fadar Shugaban Kasa. Zaman ya samu halarcin Mataimakin…

Shugaban Kasa Muhammadu Buhari na jagorantar taron Majalisar Zartarwa ta Kasa na wannan mako ta bidiyo daga Fadar Shugaban Kasa.

Zaman ya samu halarcin Mataimakin Shugaban Kasa Farfesa Yemi Osinbajo da Sakataren Gwamantin Tarayya Boss Mustapha da Shugaban Ma’aikatan Fadar Gwamnati Farfesa Ibrahim Gambari da kuma Mai Ba Shugaban Kasa Shawara Kan Tsaro Babagana Monguno.

Ministoci bakwai na halartar taron a zahiri yayin da sauran mahalarta taron ke bayar da gudunmuwa kai tsaye ta bidiyo daga wuraren da suke.

Ministocin da ke halartar taron da kansu su na Ministan Sharia’a Abubakar Malami da Ministar Kudi da Tsare-Tsaren Kas Zainab Ahmed sai kuma Ministan Ayyuka da Gidaje Babatunde Fashola.

Sauran su ne Ministan Yada Labarai da Al’adu Lai Mohammed, da Ministan Sufurin Jiragen Sama Hadi Sirika, da takwaransa na Abuja Muhammad Bello da kuma na Albarkatun Ruwa Suleiman Adamu.