Shugaban Kasa Muhammadu Buhari na jagorantar wani muhimmin taro kan harkokin tsaro tare da Mataimakinsa, Farfesa Yemi Osinbajo a Fadar Aso Rock dake Abuja.
Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya ya rawaito cewa taron dai na gudana ne a Dakin Taron Uwar-Gidan Shugaban Kasa sakamakon kwaskwarimar da ake yi a babban dakin taro na fadar shgaban.
- An mayar da Arewa maso Gabas saniyar ware a harkar titin jirgin kasa – Gwamnan Gombe
- Tallafin COVID-19: Majalisa ta kalubalanci Minista kan yadda ta kashe N32.4bn
Taron dai yana kuma samun halartar Sakataren Gwamnatin Tarayya, Boss Mustapha da Shugaban Ma’aikatan Fadar Shaugaban Kasa, Farfesa Ibrahim Gambari, Ministan Tsaro, Bashir Magashi da kuma Mai ba Shugaban Shawara Kan Harkokin Tsaro, Manjo Janar Babagana Monguno mai ritaya.
Sauran masu halartar taron sun hada da Babban Hafsan Tsaro, Janar Lucky Irabor, takwaransa na Kasa, Lafatanara Janar Ibrahim Attahiru, da na Ruwa, Bayis Admiral Auwal Zubairu da na Sama, Eya Mashal Ishiaka Oladayo Amao da kuma mai rikon mukamin Babban Sufeton ‘Yan Sandan Najeriya, Usman Alkali Baba.
Babu dai cikakken bayani kan abubuwan da taron zai fi mayar da hankali, amma ana gani ba zai rasa nasaba da irin matsalolin tsaron dake kara tabarbarewa a kullum ba.
Taron dai na zuwa ne a daidai lokacin da Najeriya ke fuskantar kalubalen tsaro a kusan kowanne bangare na kasar.