✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Buhari ya yi ganawar sirri da dan Idriss Deby

Ganawar farko bayan Janar Mahamat ya gaji mahaifinsa wanda ya rasu a filin yaki.

Shugaban Kasar Najeriya Muhammadu Buhari ya karbi bakuncin shugaban rikon kasar Chadi, Janar Mahamat, dan shugaba marigayi Idriss Deby.

Janar Mahamata Idriss wanda ya gaji mahaifinsa wanda ya rasu a fagen yaki ya isa Fadar Shugaban Kasa ne da misalin karfe 11 na safiyar Juma’a, inda suke ganawar sirri da Shugaba Buhari.

Ana ganin tattaunawar ba za ta rasa alaka da yunkunin kashen Sahel da ke makwabtaka da Najeriya ba, wajen kawo dawwamammiyar mafita ga matsalar ta’addanci kwararar makamai da ke barazana ga tsaro da zaman lafiya a yankin.

Tun kafin rasuwar Idriss Deby, Najeriya da Chadi sun dade suna kawance wajen yaki da ta’addanci.

A garin yaki da ’yan tayar da kayar baya ne Marshal Idris Deby ya samu raunukan da suka kai ga ajalinsa a watan Afrilun 2021.

%d bloggers like this: