Shugaban Kasa Muhammadu Buhari na ganawa da daliban Makarantar Sakandaren GSSS Kankara, Jihar Katsina da suka shaki isakar ’yanci bayan makonsu guda a hannun masu garkuwa da mutane.
Hadimin Shugaba Kansa kan Kafafan Sadarwa na Zamani, Bashir Ahmad ya sanar cewa: “Shugaban Buhari zai gana da daliban GSSS Kankara a yammacin Juma’a a Jihar Katsina.”
- Aisha Buhari ba ta ce komai kan Daliban Kanakara ba
- COVID 19: Gwamnan Sakkwato yana neman addu’a
- Daliban Kankara sun sauka a Gidan Gwamnatin Katsina
Ganawar ta su da daliban tana zuwa ne washegarin ranar da ’yan bindigar sun sake su bayan sun sun yi awon gaba da su a makon jiya.
Tunda farko Buhari ya bayyana farin cikinsa da sakin su da aka yi a ranar Juma’ar da ta gabata, 11 ga watan Disambar 2020.
“Ina maraba da sakin daliban Makarantar Sakandiren Kimiyya ta Kankanra. Hakika sakin su zai kwantar da hankalin jama’ar kasar nan kwarai da gaske da ma duniya baki daya.
“Al’umar kasar nan na cike da farin ciki bisa kwazo da namijin kokarin da Gwamnan Jihar Katsina, Aminu Masari, ya nuna tare da hukumomin tsaro da suka hada da sojoji da ’yan sanda da masu tara bayanan sirri,” inji Shugaba Buhari.
Buhari, ya yi bikin cikarsa shekara 78 a mahaifarsa da ke garin Daura, Jihar Katsina a wata ziyara ta musanman da ya kai garin.