✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Buhari Ikon Allah!

Wannan wake an gabatar da shi a yayin taron kungiyar Marubuta ta Najeriya (ANA), a Babban dakin Karatu na Jihar Kano, a ranar Lahadi 5-11-2017.…

Wannan wake an gabatar da shi a yayin taron kungiyar Marubuta ta Najeriya (ANA), a Babban dakin Karatu na Jihar Kano, a ranar Lahadi 5-11-2017.

 

Da sunan Rabbi Allah,

Ya Khalikul Nabiyyina,

Allahu Sarkin Halittu,

Ban basira nai bayani.

 

Salati gun Nabiyyu,

Cikamakin Annabawa Al’aminu,

Ahali nasa har sahaba,

Sahibai da tabi’una duk na sani.

 

Godiya gun Rabbani,

Sarkin da ke ba da mulki,

Ya amsa addu’armu,

Kan bai wa Buhari kasa Maliku gwani.

 

Allah ka ida nufin

Jagora shugabanmu,

Shugaban kasa Muhammadu,

Buhari mai kishin kasa na sani.

 

Shugaba da ka ba mu Rabbi,

Jajirtacce yake babu shakku,

Aiki gu nai kusa ni,

Ba dare balle da rana haka babu raini.

 

Manufar waken haskawa,

Allah karan basira, 

Za ni zayyano nassarori,

Da mugun nufi ake kar a gani.

Tsaro farkon batuna a nan Kano,

Garina zuwa yanki Arewa, 

Kudanci duk kasata baki daya,

Sauki ya samu dadai ido na gani.

 

Yanka da ake da harbi,

kona gari ga bom kuma kodayaushe,

Nasarar Allah ta hanyar Baba,

Ta tabbata daga Al-Shafi’u Rabbani.

 

Cin  hanci rashawa ya zam,

Tamkar halali da can a baya,

 Ya zamo mai cin rashawa,

Haramun shike babba ku san nan nai tuni. 

 

Yau masu murkushe tallakawa,

Wato azzaluman kasarmu,

Cikin tsoro suke kullu-yaumin,

Damuwa suke dukka rana mun gani.

 

Talakka yana ta barci har munshari,

Babu tsoro yau cikin garina,

barayin zamanin can bacci nasu,

Na wuju-wuju ga tunani da na sani. 

 

Gwamnatin dattijo namu,

Na binciken azzaluman kasata,

A kullu-yaumin cikin nutsuwa da tsari,

Aikin yake bisa dokar kasata bayani ana kara sani.

 

Gyaran da wuya na gano shugabanmu,

Ake tadewa don durkushe shi, 

Manufarsu warware dukka tsari,

Don lalata turbar gyaran kasar muna gani.

 

Kafofin sadarwar zamani,

Makiya kasa na yada farfaganda, 

Kan talakka ya yi butulci,

Ya kyamaci shugaba dan Daura munka sani.

 

Na yi imani da Allah,

Mai gaskiya bai wulakanta ko’ina,

Kuma zan bayana Muhammadu Buhari,

Badauri Alkatsinawi mai dogon hange ganina.

 

Cin hanci rashawa kasata na kusan,

Zamowa tarihi mu gane,

Ya ragu sai burbushinsa yau,

Don himma a kan matsalar daga gwamnatin ku sani. 

 

Sharrin da sukai a kullum Ilahu,

Karimu Wahid ke tarwatsawa, 

Shi ko makiya nasa na a ciki,

Da wajen gwamnatin tasa kun fa sani.

 

Batun noma na dora gadon iyaye,

Kakanni kasata Afrika duniya duk,

Watsi da akai da noma sanadin,

Talaucin kasata Arewa Afrika nawa tunani.

 

Hawan dattijo mulki noma ya samu,

Lura da gaske sosai jama’a sun kai harama,

Ga noma sun amsa kiran dattijon dukka mun gani.

 

Gonakin da sukai likimo shekaru aru,

An noma lokacin nan ’yan Najeriya,

Sun himmatu ainun don ciyar,

Da kai ba dogaro waje nai bayani. 

 

kima darajar kasata sai,

Habbaka ’yan uwana shugabannin,

Duniya kaf sun aminta,

Mun yi dacen na jagora bayani.

 

Wahalar fetur kasata tamkar,

Tarihi hakikar gaskiyar batun kam,

Ba karanci ko kwa layi har a biki,

Na Sallar Musulunci ko Kirismeti an gani.

 

Yanzu zan kara kira gare mu tallakawa,

Masu arzikinmu bai dai mutanen,

Birni da karkararmu mu yi du’a’i

Kan kasarmu hada da har Baba gwani.

 

Amma mu sani batun gaskiya,

Sai mun kishin kasarmu,

Lokacinmu ya doru bisa turbar,

Aiki ga kasarmu domin dace na ce ni.

 

Tafiyar babu sauki a yanzu,

barnar ta yi zurfi da jimawa saninmu,

karya sharri gare shi don durkushe,

kokarinsa Allah na taimako nasa ku sani. 

 

Allah karin roko gare Ka kara lafiya,

Gare shi dattijo mai amana,

Shugaban mai gaskiya ne aiki yake,

Dare da rana masu adalci sun sani.

 

Rokon karin imani basira fasaha,

Aiki a tsari kariya daga zalumanmu,

karin godiya ga Rabbi Mabuwayi,

Gagara misali Allahu Rabbani. 

 

Nan zan takaita ’yan uwana,

Allah tsare kasarmu,

Buhari kam shugaba ne,

Kuma aya ne a gare mu,

Mai hankali kadai ke da sani.

 

Alhamdulillah!