A dan takaitaccen nazarin da na yi a kan zaben shekara ta 2019 a Najeriya da farko na auna farin jinin Shugaba Muhammadu Buhari a lokacin da ba shi ke kan mulki ba da kuma bayan ya hau kan karagar mulkin kasar nan.
Tabbas duk mai tunani da nazari ya kamata ya san cewa idan Buhari yana da kashi 90 bisa 100 na masoya a Najeriya kafin a yi zaben 2015, to a yanzu bai fi ya tsira da kashi 50 cikin 100 daga cikin masoyansa ba, saboda idan muka yi la’akari da magoya bayan Shugaba Muhammadu Buhari a Najeriya to za mu ga mafi yawancinsu talakawa ne wadanda ba su da abincin yau ballantana na gobe.
Wannan sharhi nawa ya zo ne biyo bayan ji da ganin ra’ayi jama’a da dama wadanda muke mu’amula da su a fili ko ta hanyar yanar gizo wato Internet ta hanyar yin amfani da maganganun da mutane ke yi a fili ko kuma shafukansu na sada zumunta. Idan Buhari yana samun kashi 90 bisa 100 na yabo a da, to a yanzu ba ya samun fiye da kashi 50 cikin 100 daga wajen ’yan kasa saboda mafi yawanci talakawan da suke yabon Buhari kuma suka yi imani har zuciyarsu cewa Shugaba Buhari zai magance matsalar da ke damunsu to yanzu sun cire tsammanin hakan daga gare shi, domin ganin yadda talaka a Najeriya ke cikin halin tsadar rayuwa musamman ma ta bangaren tsadar kayan masarufi kuma ga fama da rashin aikin yi. Sannan abin da gwamnatin Najeriya a karkashin jagorancin Shugaba Buhari ta fake da su su ne yaki da cin hanci da rashawa da kuma samar da tsaro, wanda kuma su ma a yanzu za mu iya cewa an koma ’yar gidan jiya domin idan muka dubi bangaren cin hanci da rashawa za mu ga cewa gwamnatin ta kwato makudan kudade daga hannun barayin gwamnati amma har yanzu talakan kasar nan bai san me aka yi da wadannan kudaden da aka karbo ba.
Ta bangaren tsaro kuwa mayakan Boko Haram har yanzu suna cin karensu babu babbaka. Ga rikicin makiyaya da manoma, ga rikicin Zamfara. To a shawarce muddin ShugabaBuhari ba zai daina biye wa wadannan mutum 4 da ke karkashinsa kuma suke hana shi rawar gaban hantsi ba, to sai farin jininsa ya kara ja baya daga kashi 50 zuwa kashi 30 duk da cewa ba zan fadi sunayen wadannan mutane ba saboda tsaro, amma da yawan ’yan Najeriya sun sansu.
Buhari zai iya lashe zaben 2019 amma sai ya yarfe gumi daga goshinsa saboda da dama daga cikin ’yan kasa da suka yi tsammanin Buhari zai warware musu matsalolinsu, to yanzu sun dawo daga rakiyarsa.
Allah Ya zaba mana mafi alheri a kasar nan, amin.
Naku Prince Ya’u Adamu Bulkachuwa, Jihar Bauci
09034444404 ko 09066738686