✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Buhari ba shi da tausayi, ya yi murabus kawai —Tsohon hadimin Ganduje

Tsohon hadimin ya ce Buhari ya gaza kare rayuna ’yan Najeriya

Tsohon hadimin Gwamnan Jihar Kano, Salihu Tanko Yakasai, ya yi kira ga Shugaban Kasa Muhammadu Buhari da ya sauka daga mulki.

Yakasai, wanda Ganduje ya sallama daga aiki saboda irin wadannan kalaman a baya, ya wallafa a shafinsa na Twitter cewar Buhari ya sauka daga mulki, saboda harin ’yan bindiga suka kai kan jirgin kasan Abuja zuwa Kaduna.

“Shugaba Buhari, gwamnatinka ta gaza. Za mu ci gaba da yi maka tuni a kan wannan. Ina kira da da ka yi murabus! idan ba za ka iya ba mu kariya ba, ba ma bukatarka ko kadan.

“Ba ka da tausayi, ba ka da jinkai sannan ba ka dauki rayuwarmu bakin komai ba.

“Duk lokacin da aka kashe ’yan Najeriya, Shugaba Buhari ta hannun Garba Shehu da Femi Adesina za su fitar da sanarwar taro a Villa. Wasu lokutan ana daukar mataki amma ba a tabbatar da an magance matsala, haka abun ke ci gaba. Ba za mu yarda hakan ya ci gaba da faruwa ba.

“Muna cikin bacin rai, ba abin da mu ke so sai Buhari ya yi murabus. A bayyana yake ba za ka iya kare rayukanmu ba. Ba ma jin za ka iya ba mu kariya tun daga gidajenmu zuwa kan hanyoyi. Ran mu ya baci, mun gaji kuma ba za mu iya ci gaba a haka ba,” kamar yadda ya wallafa.

Tsohon dan jam’iyyar na APC, ya  ce Buhari ya gaza tsare rayukan ’yan Najeriya.

Tuni dubban jama’a suka shiga korafi da koke-koke kan yadda ’yan bindiga ke daukar rayukan mutane kullum a Najeriya.