✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Bugun zuciya ya kashe Minista a Gabon

Ministan ya rasu sakamakon bugun zuciya

Ministan Harkokin Wajen Kasar Gabon, Michael Moussa Adamo ya rasu sakamakon bugun zuciya.

Ya gamu da ajalin nasa ne a lokacin da yake jiran shiga taron Majalisar Ministocin Kasar, kamar yadda majiyar Shugaban Kasar ta sanar.

Moussa, mai shekara 62, wanda ya dade yana goyon bayan Shugaba Ali Bongo Ondimba, ya kamu da ciwon zuciya kuma ya mutu duk da kokarin da kwararru suka yi na ceto rayuwarsa, in ji wata sanarwa da gwamnatin kasar ta fitar.

“Ya zauna a dakin jiran mutane kafin a fara taron Majalisar Ministocin a gaban wasu takwarorinsa ya fara rashin lafiya,” in ji wata majiya da ta shaida wa Kamfanin Dillancin Labaran Faransa (AFP).

An kai shi asibitin sojoji, wanda ya rasu da misalin karfe 11 na safiyar ranar Juma’a.

Da yake mayar da martani game da mutuwar, Shugaban Kasar, ya bayyana marigayin a matsayin “babban jami’in diflomasiyya, kuma mutum mai gaskiya.”

“A gare ni, aboki ne, mai aminci da rikon gaskiya, wanda kodayaushe nake iya dogara da shi. Babban rashi ne ga Gabon,” in ji shi.

An haifi Moussa Adamo a garin Makokou da ke Arewa Maso Gabashin kasar a shekarar 1961, kuma ya fara gabatar da shirye-shirye a gidan talabijin na kasar.

A shekara ta 2000 an nada shi Ministan Tsaron kasar.

Lokacin da aka zabi Bongo a matsayin shugaban kasa bayan rasuwar mahaifinsa, Omar Bongo Ondimba a 2009, Moussa Adamo ya kasance mai ba shi shawara na musamman.

Bayan shafe shekara 10 a matsayin Jakadan Gabon a Amurka har zuwa 2020, an nada shi Ministan Harkokin Wajen Kasar a watan Maris, 2022.