✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Budurwa ta kashe kanta saboda fitar da Brazil a gasar kofin duniya

Wata yarinya ’yar kimanin shekara 15 mai suna Pragya Thapa da ta fito daga Nepal ta sagale kanta da igiya a wata bishiya har lahira…

Wata yarinya ’yar kimanin shekara 15 mai suna Pragya Thapa da ta fito daga Nepal ta sagale kanta da igiya a wata bishiya har lahira jim kadan bayan kasar Jamus ta yi kaca-kaca da Brazil da ci 7-1 a gasar cin kofin duniya da aka gama a makon jiya.
Ita dai yarinyar, rahotanni sun tabbatar ’yar-gani-kashenin Brazil ce, ta samu matasala ce jim kadan bayan an kammala wasan.  Hasalima ba kasar Brazil din ta ziyarta don kallon yadda wasan ya kaya ba, ta kalla ne a akwatin talabijin a gidansu da ke Nepal garin da ke makwabtaka da Indiya.
Kamar yadda jami’an tsaron Nepal suka tabbatar, da farko yarinyar ba ta dauki al’amarin da zafi ba, amma ganin yadda kawayenta suka rika zolayarta a kan lallasawar da aka yi wa Brazil ce ta sa ta yanke shawarar kashe kanta don ta huta da bakin ciki.
Marigayiyar da ke ajin karatu na 10 a wata makaranta an tabbatar ta dauki ranta ne don ta huta da bakin cikin zolayar da kawayenta suke mata a kan lallasa Brazil da aka yi a gasar cin kofin duniya.
Tuni jami’an tsaron kasar suka ce sun fara gudanar da bincike a kan al’amarin don ganin irin haka ba ta sake faruwa ba.