Wata budurwa ta bude wa wasu mata biyu wuta a rikicin da ya barke a Gundumar Ofoni, mahaifar Mataimakin Gwamnan Jihar Bayelsa, Lawrence Ewhrudjakpo.
Wani ganau ya shaida wa Aminiya cewa wasu mata su uku a yankin sun harbi wata budurwa da bindiga saboda sabanin da ya shiga tsakani, lamarin da ya kawo tsaiko ga sha’anin zabe a yankin.
- Na gamsu da yadda ake gudanar da zabe a Gombe —Makaman Cham
- Shugaban PDP a Abuja ya rasu a ranar zabe
A cewarsa, bayan harbin, harsashin ya tafi ya sake ji wa mata mata rauni wadda aka garzaya da ita asibiti.
An ce jama’ar da ke wurin sun kama ’yan daban su uku da suka tada fitinar tare da mika su ga jami’an tsaro.
Daga bisani kura ta lafa a yankin, inda aka ga Mataimakin Gwamnan ya zo ya kada kuri’arsa a Rumfar Zabe ta 6 a Gunduma ta a Ofoni.
Ewhrudjakpo ya yi kira ga mutanen yankin da a guji tada fitina, saboda a cewarsa sai da sahihin zabe ake samun ci gaba.
Ya zuwa hada wannan labari, an kira kakakin ’yan sandan Jihar Bayelsa, SP Asinim Butswat, domin jin ta bakinsa kan batun amma bai daga kira ba.