Bayan gaisuwa, na lura sosai cewa tun shigowar watan azumi yawan hare-haren da kuke kaiwa ya ragu matuka musamman a jihohinmu na Katsina da Zamfara da Sakkwato da Kebbi da Neja.
Ba kamar Kaduna ba da har yanzu ake samun rahoton matsaloli nan da can. Wadannan jihohi namu sun samu zaman lafiya daidai gwargwado don bauta wa Allah da gabatar da ayyukan ibada cikin natsuwa.
Ni dai ban ji rahotannin kashe mutane ko kama su ba kamar yadda aka saba.
Allah Ya sani tunanina yana ba ni cewa ba wani mataki da gwamnati ta dauka ne ya hana ku kai hare-haren ba, ba kuma murkushe ku aka yi ba, kuma duk kokarin da gwamnati take yi ba a samu cikakkiyar nasarar da za ta hana ku iya kai farmaki musamman a kauyuka ba.
Abin da nake zato shi ne da kanku kuka zabi ku sassauta watakila saboda alfarmar wannan wata na Ramadan. Idan haka ne hakika to ina yaba muku, ina jinjina muku kuma ina gode muku.
Wannan ya nuna har yanzu akwai sauran alheri komai kankantarsa a zukatanku.
Sai dai abin da nake so in jawo hankalinku game da shi, shi ne idan kuna tunanin watan Ramadan yana da alfarma to lallai ku sani rayukan Musulmi suna da alfarma a watan Ramadan da bayan watan Ramadan kuma WALLAHI TALLAHI ran mutum Musulmi ya fi watan Ramadan alfarma kuma ya ma fi Dakin Ka’aba kamar yadda Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasallam) ya nuna.
Saboda haka nake kira gare ku da ku girmama wannan alfarmar a kowane lokaci.
Ina yin kira na musamman gare ku da ku tuba ku daina kashe rayukan bayin Allah ba ji ba gani.
Na sani kuna cewa dalilinku na daukar makami shi ne zalunci da aka yi ta yi muku tsawon lokaci kuma hukuma ba ta yi komai a kai ba, saboda haka kuke daukar wa kanku fansa.
To ina so ku sani ana daukar fansa ce kawai a kan wanda ya yi maka laifi kuma an ba ka da dama ka kare kanka ko ka rama daidai abin da aka yi maka.
Amma kamar yadda kuka sani hare-harenku suna rutsawa da wadanda babu ruwansu kuma ba su yi muku laifin komai ba. Irin wadannan su ne ma suka fi yawa.
Hakika yin hakan zalunci ne kuma Allah zai yi hukunci a kai Ranar Alkiyama.
A matsayina na Musulmi dan Arewa kuma na san ’yan Arewa ne kuma kuna cewa ku Musulmi ne, ina nanata kira gare ku cewa ku tuba ku koma ga Allah ku daina zubar da jinin haka.
Kuma ko da wasa kada wani a cikinku ya yi tunanin laifinsa ya yi yawan da Allah ba zai karbi tubarsa ba. Ko kadan!
Malamanmu sun karantar da mu Hadisin wani mutum da ya kashe adadi mai yawa na mutane amma daga karshe da ya so ya tuba aka ce ya tafi wani gari ya tuba a can.
An ce ajalinsa ya riske shi a kan hanya inda mala’ikun azaba da na rahama kowanne suka zo karbar ransa.
Da aka duba sai aka ga cewa ya fi kusanci da garin da zai je ya tuba da dan taki kadan wanda hakan ya sa mala’ikun jinkai suka karbe shi duk da cewa bai karasa ya tuba din ba.
Ku sani ba wani zunubi da ya gagari tuba a wurin Allah. Idan aka yi tuba ingantacciya Allah zai yafe komai ya zama kamar ba a yi ba.
Tuba ingantacciya ita ce mutum ya yi nadamar abin da ya aikata kuma ya kudirce a ransa tsakani da Allah ba zai sake ba, idan kuma akwai kayan mutane a hannunsa ya dawo musu da abinsu.
Hakika kashe rayuka ba karamin laifi ba ne kamar yadda Allah Ya bayyana a Alkur’ani kuma Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasallam) a hudubarsa ta karshe ya nanata wajabcin kiyaye dukiyar mutane da rayukansu da mutuncinsu kuma ya ce suna da alfarma matuka.
Ashe ke nan wanda zai rika keta alfarmarsu yana fito-na-fito da Allah ne da ManzonSa. Ina rokon Allah Ya kiyaye ku jidali da Manzon Allah Ranar Lahira saboda yadda kuke keta alfarmar rayukan al’ummarsa.
Na sani cewa koyaushe kuka yi yunkurin ajiye makamai kuna cewa gwamnati tana saba muku alkawari.
To ina ba ku shawara ku samu nagartattun mutane da za su shiga tsakani yadda za a tabbatar kowane bangare ya cika alkawarin da ya dauka.
Abu mafi muhimmanci shi ne ku sani cewa daina kashe mutane shi ne alheri a gare ku duniya da Lahira. Saboda haka ko ba ku samu irin hadin kan da kuke so daga gwamnati ba, bai kamata ku ci gaba ba.
Za ku tuba ne saboda Allah ba saboda gwamnati ba.
Ina addu’ar Allah Ya sa wannan wasika idan ta isa gare ku ku tsaya ku yi nazari a kanta sosai kuma ku yarda ku tuba daga kisan mutane saboda mu gudu tare mu tsira tare.
Na gode sosai Daga Ibrahim Siraj Adhama, Tsangayar Koyon Aikin Jarida, Jami’ar Bayero, Kano. Imail: [email protected]