Shugaban Kasar Somalia, Hassan Sheikh Mohamud ya tabbatar da cewa akalla mutum 100 ne aka kashe sakamakon wasu hare-haren kunar bakin wake biyu da aka kai da motoci a wajen Ma’aikatar Ilimi ta kasar.
An kai harin ne a ranar Asabar a Mogadishu, babban birnin kasar, inda akalla mutum 300 suka samu raunuka daban-daban.
Mista Mahmud ya kai ziyara wurin da aka kai harin inda waɗanda suka shaida lamarin suka bayyana cewa cikin mintoci kaɗan motocin suka kaddamar da hare-haren.
Shaidu sun bayyana cewa ita motar ta biyun ma ta kai harin ne a yayin da jama’a suka garzayo da kuma motar daukar marasa lafiya domin kai agaji.
Babu wata kunigiya da ta dauki nauyin kai harin zuwa yanzu amma kungiyar al-Shabab da ke da alaka da Al-Qaeda ta sha kaddamar da irin wadannan hare-hare.
Kungiyar ta al-Shabab ta yi sanadin mutuwar dubban mutane a kasar ta Somalia da kuma raba miliyoyi da muhallansu.
A ’yan kwanakin nan gwamnatin kasar ta rika zafafa hare-hare kan ’yan kungiyar, lamarin da ya jawo ita ma kungiyar ke zafafa hare-hare.
Ko a kwanakin baya sai da kungiyar ta kai hari a wani otel inda ta kashe mutane da dama.