✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Bolibiya ta soke wasan sada zumunta da Najeriya

kasar Bolibiya ta janye daga halartar wasan sada zumunta da Najeriya da ake sa ran zai gudana a garin Uyo a ranar Alhamis 26 ga…

kasar Bolibiya ta janye daga halartar wasan sada zumunta da Najeriya da ake sa ran zai gudana a garin Uyo a ranar Alhamis 26 ga watan nan da muke ciki.

kasar ta ce ta soke ziyartar Najeriya don yin wasan ne saboda matsalar tsaro kuma ta ga ana saura kwana uku kenan a gudanar da zabe a Najeriya.
Kamar yadda shugaban hukumar kwallon kafa ta Boliya (FBF) Misra Carlos Chabez ya sanar, ya ce “matsalar tsaro da kuma ta zabe a Najeriya ce ta sa muka yanke shawarar kin halartar wasan”.
Sai dai kasar tana yunkurin ganin Najeriya ba ta kai ta kara gaban Hukumar FIFA ba don ganin ta biya ta kudaden da ta kashe a shirye-shiryen wasan.
Sai dai da yawa daga jaridun Najeriya sun buga labarin Najeriya za ta yi wasan sada zumunta da Bolibiya a ranar Talatar da ta wuce.
A ranar Lahadi 29 ga wtaan nan ne kuma ake sa ran kungiyar kwallon kafa ta Najeriya Super Eagles za ta yi wasan sada zumunta da Afirka ta Kudu.