✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Bola ta rufto ta kashe mutum 17 a Mozambikue

Akalla mutum 17 aka tabbatar da mutuwarsu, ciki har da kananan yara a birnin Maputo da ke kasar Muzambikue, wasu da dama kuma suka jikkita…

Akalla mutum 17 aka tabbatar da mutuwarsu, ciki har da kananan yara a birnin Maputo da ke kasar Muzambikue, wasu da dama kuma suka jikkita a lokacin da bola ta rufto a kansu.

Hukomomi a yankin sun ce wata bola da ta yi tsawon mita 15 ita ce ta rufto, a lokacin da ake tafka ruwan sama.

Wurin da bolar ta ke dai, matsugunin daruruwan matalauta ne da suka gina dakunansu da langa-langa ko katako kamar yadda BBC ta ruwaito.

Kwasam sai bolar ta rufta ta bi ta kan wasu gidaje biyar da ke gefenta a sanadiyar ruwan sama.

Ma’aikatan ceto na ci gaba da tona bolar ko za su sake samun wasu mutane ko kayan da lamarin ya rufta da su.

Mai magana da yawun hukumar agajin gaggawa, Leonilde Pelembe, ya yi gargadin a yi taka tsantsan don ta yiwu akwai karin mutanen da bolar ta danne.

‘’Bayanan da muka samu daga hukumomin yankin sun ce mutanen da suke zaune a wurin bolar sun fi wadanda aka ba mu bayanin sun mutu, ‘’ in ji Mista Pelembe.

Gundumar Hulene da ke Maputo, daya ce daga cikin wuraren da ba a damu da su ba a birnin. Yawancin mazauna gundumar su na samawa kansu matsuguni ne ko dai a can saman bolar ko kuma a gefe, ciki kuwa har da kananan yara.

Bolar ba wai ta na zame musu hanyar samun abinci ba ce kadai, har ta kan zama sanadin samun kudaden shiga kamar yadda wakilin BBC Jose Tembe ya bayyana.

Wakilin BBC ya ruwaito cewa tun ya na karami ya taso ya ga bolar a wurin, a shekarar 1980.

Hakanan kuma an ruwaito cewa lokuta da dama, hukumomin yankin sun yi ta kokarin korar mutane tare da kwashe bolar. Duk lokacin da damuna ta kama, jami’ai na zuwa tare da bai wa mutanen wurin wasu filaye don su bar inda suke.  Amma da zarar damuna ta wuce, mutanen sai su sake dawowa. 

Nan ne wurin da ya fi musu kusa da birni, da samun kayan ‘Jari bola’ don saidawa, wasu lokutan kuma sukan samu kayan abinci na gwangwani da manyan shaguna suke zubarwa don lokacinsu ya wuce. Ko dai don su ci, ko kuma saidawa.

Gwamnati ta sha daukar alkawarin za ta rufe wurin bolar baki daya, amma har yanzu hakan ba ta samu ba.

Rashin rufe wurin ya sanya, har yanzu mutane su na zaune a yankin.

Kamfanin dillancin labarai na Reuters ya ruwaito cewa, hukumomin sun ce a baya sun ce mazauna yankin su fice daga nan saboda gine-ginen da suka yi ba bisa ka’aida ba ne amma shiru babu alamun za su tashi.

Wani mazaunin yankin da dansa ya ji rauni sakamakon zaftarowar bolar, ya shaidawa BBC cewa ba shi da wurin da zai koma idan ya bar unguwar, kuma ya ce idan gwamnati ta bukaci su koma wani wuri da suka tallafa musu ginanne babu abin da zai sa ya ci gaba da zama a wurin mai cike da hadari.

An sheka ruwan sama kamar da bakin kwarya ne a brnin Maputo tun daga ranar Lahadi da ta gabata, hakan ne ya janyo ambaliyar ruwa da ya lalata gidajen jama’a.