✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Boko Haram: ‘Yan asalin Borno da Yobe mazauna Abuja sun ziyarci Gwamna Zulum

‘Yan asalin Jihar Borno da Yobe da suka hada da dattawa da mambobin majalisa da tsofaffin ministoci da manyan jami’an Gwamnatin Tarayya sun kasance a…

‘Yan asalin Jihar Borno da Yobe da suka hada da dattawa da mambobin majalisa da tsofaffin ministoci da manyan jami’an Gwamnatin Tarayya sun kasance a Maiduguri a  ranar Lahadin da ta gabata, inda suka  gana da Gwamna Babagana Umara Zulum na Jihar Borno.

Taron wanda ya gudana a Gidan Gwamnati Jihar an yi shi ne domin tattaunawa kan matsalolin tsaron da jihar ke fama da shi da ya danganci rikicin Boko Haram.

Ayarin wanda tsohon Ministan Birnin Tarayya Abuja Alhaji Ibrahim Bunu ya jagoranta, ya kasance irinsa na farko da ’yan asalin Jihar Borno mazauna Abuja suka kai ziyara, domin bada shawarwari kan matsalar tsaro da jihar take fama da ita.

Gwamna Zulum, ya bayyana farin cikinsa ga ayarin bisa ziyarar.  “Na yi matukar farin cikin karbarku da wannan maraice. Ba sai na yi muku maraba da zuwa Jihar Borno ba, saboda ku ’yan gari ne,” inji shi.

Gwamna Zulum ya jinjina wa himmar  Shugaban Kasa kuma Babban Kwamandan Askarawan Najeriya Muhammadu Buhari wajen maido da zaman lafiya a Jihar Borno.

“Muna godiya da kula ta musamman da Shugaba Muhammadu Buhari ya bayar kan samar da zaman lafiya da tsaro da sake gina Jihar Borno,” inji Zulum.

Ya kara da cewa “Kalubalen masu tayar da kayar baya da muka fuskanta ya samu kula sosai tare da tattaunawa da Shugaban Kasa yayin ziyarar aiki a Maiduguri. Bari in fada muku, cewa sojojinmu suna yin aiki yadda ya kamata a yakin da suke yi da ’yan ta’addar. An samu kyakkyawar jituwa tsakanin sojoji da sauran jami’an tsaron da suke aiki tare da sauran fararen hula.

“Muna ganin ci gaba a fannin dabarun aiki da tura kayan aiki da shawarwari tun bayan harin Auno. Muna da yakinin cewa da yardar Allah za mu ci nasara a wannan yaki tare da maido da zaman lafiya a jiharmu,” inji Zulum.

Gwamna Zulum ya ce duk da kalubalen da aka samu tun farko gwamnatinsa ta aiwatar da ayyukan ci gaba da yawa.

Tun farko a jawabin Alhaji Ibrahim Bunu ya mika jajensu ga al’umma da gwamnatin Jihar Borno. “Mun ga irin himmarka da kwazo da kake nunawa wajen hidima ga al’ummarmu,“ inji  Bunu.