Mayakan Boko Haram sun kai farmaki sansanin sojojin Kamaru a ranar Asabar inda suka kashe mutum bakwai tare da raunata da dama.
Sun kai harin a sansanin soji da ke Sagme a yammacin ranar Asabar kamar yadda sojoji suka sanar.
- Bayan karbar kudin fansa, ’yan bindiga sun ki sako Daliban Tegina
- ’Yan sanda sun kubutar da mutum 8 daga hannun masu garkuwa a Katsina
Maharan, dauke da muggan makamai sun yi shigar burtu da kakin soja a ababen hawa shida.
Bayan share awanni ana artabu da su, mayakan sun kashe kwamandan sojojin tare da dakarunsa shida.
“Sojojin sun yi namijin kokari wajen daukar lokaci suna artabu da ’yan ta’addan.
“Dole a jinjina musu kan yadda suka yi kokarin dakile harin tare da ceto rayukan wasu da dama,” a cewar wani da ya bukaci a sakaya sunansa.
Rundunar sojin ta ce ta jikkata da dama daga cikin mayakan amma ba ta bayyana adadinsu ba.
Harin na ranar Asabar na daga cikin mafiya muni da aka kai wa rundunar sojin Kamaru cikin wata 10 da suka wuce, a cewar rahoton rundunar sojin kasar.
Tun a shekarar 2014 Boko Haram take kai hari a Arewacin kasar Kamaru, inda ta kashe akalla mutum 2,000, a cewar rahoton rundunar.