✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Boko Haram sun kai hari Miduguri

Rahotannin na nuna cewa ‘yan Boko Harm sun shigo cikin garin Maiduguri inda suka kai hari a yankin Polo ta Molai da misalign karfe 5:…

Rahotannin na nuna cewa ‘yan Boko Harm sun shigo cikin garin Maiduguri inda suka kai hari a yankin Polo ta Molai da misalign karfe 5: 25 na yamman ranar Alhamis.

Sun ta yin harbe-harbe, wanda hakan mutanen garin suka arce domin a cewar mutanen, sojoji ma arcewa suka yi maimaikon su tsaya su kare su.

 

Wani mazaunin Njunmari mai suna Abdul Manga ya ce sojoji ba su kawo dauki cikin lokaci, “da misalin karfe 5:25 suka shigo. Farko mun fara jiyo harbe-harbe ne, mun zata sojoji ne, sai daga baya muka sojoji na gudu, shi ne mu ma muka ara na kare. In takaice maka labarai, tare muka hau  KEKE NAPEP da wani soja domin mu gudu mu tsira.”