Gwamnatin Birtaniya ta kwace wani jirgin kashin kai na wani biloniya kuma attajiri dan kasar Rasha, Eugene Shvidler, a hanyarsa ta zuwa Dubai.
Eugene Shvidler aboki ne ga mai kungiyar kwallon kafa ta Chelsea, Roman Abramovich — wanda saboda kahon zukar da gwamnatin Birtaniya ta kafa mishi ya sa kulob din a kasuwa — kuma su biyun makusanta ne ga gwamantin shugaban kasarsu, Vladimir Putin.
- Kamfanonin jirage sun dakatar da ayyuka kan tsadar mai
- Zelensky ya saduda: Ukraine ta hakura da shiga kungiyar NATO
Birtaniya ta kwace jirgin — Bombardier Global 6500 jet — ne bayan ta sanya karin takunkumai ga manyan mutanen Rasha masu kusanci da Gwamnatin Putin kan mamayar da Rasha ta yi wa Ukraine.
Ministan Sufurin Birtaniya, Grant Shapps, ya sanar ta shafinsa na Twitter cewa, “Za mu gurgunta makusantan Putin har sai sun kasa ci gaba da rayuwa yadda suka saba, saboda yadda dubban mutane ke rasuwa.”
Jirgin shi ne na farko da Birtaniya ta kwace karkashin sabuwar dokar takunkunmin da gwamantin kasar ta kakaba wa makusantan Gwamnatin Putin.
Wani jami’in gwamnatin Birtaniya ya ce an tsare jirgin ne a ranar Talata, bayan saukarsa a filin jirgi na Farnborough, a lokacin da Eugene Shvidler ke kan hanyarsa ta zuwa Dubai, yanzu sai dai Shvidler “ya karasa tafiyar tasa ta wata hanya”.
Ya ce za a bar jirgin ya wuce ne kawai idan aka tabbatar shi ko mai shi ba su da alaka Gwamnatin Putin.
Da farko ya haramta wa jirgin shiga kasar ne, daga bisani kuma ya ba da umarnin tsare jirgin a Farnborough da ke Kudancin Ingila, bayan haramta wa jirgin tashi da daukar fasinja.
Ma’aikatar Sufurin ta ce, “Gwamnatin Birtaniya ta ba da umarin hana wani jirgi da ake takaddama a kansa tsahi daga filin jirgi na Farnborough.
“Jirgin zai ci gaba da kasancewa a tsare a yayin da muke bincike domin tababtar da ko yana daga cikin wadanda dokar ta haramta saboda alakarsu da Rasha.”
Shapps ya kuma sanar da sabuwar dokar da ta ba shi hurumin tsare jirgin da ake takaddamar a kai tare da umartar Hukumar Sufurin Jiragen Sama ta kasar da ta soke lasisin duk jiragen da mukarraban gwamantin Rasha suka mallaka a Birtaniya.
A makon jiya ne wani jirgin kashin kai mallakin Abramovich ya tashi daga filin jirgi na Stansted zuwa kasar Switzerland, bayan nan ne gwamnatin Birtaniya ta kafa sabuwar dokar.