✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

“Bikin Tuna Abubakar Imam: Abin da ya sa ALQALAM za ta karrama Dokta Bukar Usman da sauransu”

A yau ne Ranar Marubuta ta Duniya, Kungiyar Marubuta ta ALKALAM Kaduna ta shirya kwarya-kwaryan biki domin tunawa da marigayi Dokta Abubakar Imam da zai…

Dokta Bukar Usman OON Da Farfesa Abdallah Uba AdamuA yau ne Ranar Marubuta ta Duniya, Kungiyar Marubuta ta ALKALAM Kaduna ta shirya kwarya-kwaryan biki domin tunawa da marigayi Dokta Abubakar Imam da zai gudana a gobe Asabar. Kungiyar za ta karrama wasu fitattun marubuta da masu yi wa Adabin Hausa hidima da suka haxa da Dokta Bukar Usman da Farfesa Ibrahim Malumfashi da Farfesa Abdallah Uba Adamu da sauransu. A tattaunawarsa da Aminiya, Uban Kungiyar, Malam Mahmoon Baba Ahmad ya bayyana dalilin shirya bikin da kuma karrama waxannan fitattun masu yi wa Adabin Hausa hidima. Ga yadda tattaunawar ta kasance:

Ko za ka yi mana bayani dangane da Kungiyar Marubuta ta Alkalam?

An kafa Kungiyar Alkalam ta marubuta Hausa ce a Kaduna a watan Afrilun shekarar 2012, don xaukar matakan magance matsalolin da ke addabar marubuta littattafan Hausa da kuma yadda za a inganta hanyoyin samar da su. Marubuta littattafan Hausa, musamman ma matan aure da ake yawan karanta ayyukansu a gidajen yaxa labarai, ba su samun sukunin kai littattafansu ma’aikatun talifi ta yadda za a kyautata rubutun da suka yi ta hanyar da ta dace da ka’idojin rubutun Hausa, sa’annan kuma a wallafa shi yadda ya fi kamata a siga mai ma’ana, kuma mai kyau da ban sha’awa. Dangane da haka ne wannan kungiya ta Alkalam ke taimaka wa marubuta da shawarwarin inganta hanyoyin rubutunsu, ta hanyar samar da malaman Hausa a manyan makarantun sakandare don su dudduba ayyukansu da niyyar gyara tsarin rubutun don dacewa da ka’idoji da sharuxxa rubutun Hausa da ake kira orthrography a Turance, sa’anan kuma a shawarce su game da hanya mafi dacewa wajen xabi’in aikinsu ba tare da wata wahala ko tsadar sayen kayayyakin aiki ba. Haka nan akwai kuma matsala ta sadar da littattafan da aka wallafa ga jama’an da ke bukata, wacce ke yawan damun marubuta, walau dai yayin da suka kai littattafansu sayarwa a kasuwanni ko kuma idan sun tashi neman kuxaxen littafan da aka sayar. Wannan ne ya sa kungiyar ta kafa wani kamfanin talifi da wallafa da ake kira Fasaha Publishing Company, ta kuma yi masa rijista da Corporate Affairs, watu hukumar da aka xorawa nauyin yin rajistar kamfanoni da ke Abuja don taimakawa wajen wallafe-wallafen ayyukan marubutan kungiyar. Haka nan kuma ana nan ana yin kyakkyawan shirin da zai taimaka wajen dillancin littafan da ’yan kungiyar suka samar a assan kasar nan ba tare da wata wahala ba.
Ko za ka yi mana bayani dangane da wannan biki na tunawa da marigayi Abubakar Imam? Waxanne abubuwa za a gabatar a yayin bikin?
Ita dai wannan kungiya kan shirya aikace-aikace a duk shekara idan Ranar Marubuta ta Duniya ta zagayo, watau 3 ga Maris, yayin da ’yan kungiyar sukan taru a wuri guda tare da ’ya’yansu da ke makaranta, waxanda za a nemi su karanta wasu shafukka daga littattafan Hausa da mashahuran marubuta suka wallafa, daga bisani kuma a sanya sa’o’insu su yi tambayoyi game da abubuwan da suka karanta don sauran su bayar da amsa. Ta haka ne ake gane fasahar yaran wajen gane dabarun rubuce-rubucen da suke karantawa. To ba wannan ne ba kaxai abin da ake yi a Ranar Marubuta ba, akan kuma sa yara yin wasu wasannin kwaikwayo game da wasu labarun da aka wallafa a littafai daban-daban da kuma rera rubutattun wakoki don kara kaifin basisarsu ta fahimtar abubuwan da aka rubuta, suke kuma karantawa. To a bana sai ’yan kungiyar suka bukaci yin wasu abubuwan da suka xara haka muhimmanci don karfafa gwiwar marubuta littattafan Hausa a ko’ina a faxin duniyar harshen Hausa. Shi ya sa aka Bullo da tsarin zakulo wani marubucin da ya yi fice a kowace shekara don a karrama shi, a kuma nuna muhimmancin ayyukan da ya yi wajen haBaka rubutun littattafan Hausa da irin gudunmawar da hakan ya bayar da ciyar da kasa gaba da kuma wayar da kawunan al’ummomin cikinta. Akwai kuma wani shiri na bayar da kyaututtuka ga waxanda suka yi fice a rubutun littattafai cikin Bangarori huxu na Adabin Hausa da za a rika bayarwa kowace shekara. Za a fara wannan tsarin ne da Marigayi Dokta Abubakar Imam Kagara a matsayinsa na mutumin farko da ya fara wallafa littafin Hausa kuma Editan farko na jaridar Hausa, Gaskiya Ta Fi Kwabo. A sakamakon haka ne kuma aka fito da tsarin bayar da kyaututtukan da aka ambata da sunansa, watau Dr. Abubakar Imam Merit Awards in Hausa Literature, a kowace shekara. Wannan Rana ta Marubutan Duniya, watau rana irin ta yau Juma’a, ’yan kungiyar sun shiga cikin bukukuwan murnar zagayowarta tare da ’yan uwansu na kasashen duniya. Sun kuma kai ziyara Birnin Zazzau, inda aka fara assasa ayyukan talifi da wallafa da kuma xab’in littafan Hausa. Sun ziyarci Unguwar Malamai a Kofar Tukur-Tukur, inda aka fara kafa Ofishin Talifi a shekarar 1936, bayan an komo da shi can daga gidan wani Bature, Hans Bischer da ake kira Xanhausa; sun kuma ziyarci Gaskiya Corporation Zaria, inda aka fara xab’in littattafan Hausa a 1939 da kuma Ofishin NORLA da aka kafa a 1952 don wallafa da kuma xab’in yawancin littattafan farko da suka xaukaka martabar rubutun Hausa. An kuma kai ziyara gidan mashahurin mawallafin Hausa, Dokta Abubakar Imam da ke Tudun Wada Zaria. A kashegari, watau ranar huxu ga wata ne kuma aka shirya yin wani gagarumin bikin murnar zagayowar wannan ranar a Arewa House, Kaduna.
Na samu bayanin cewa a yayin taron za a karrama wasu fitattun mutane, musamman marubuci Dokta Bukar Usman. Ko za ka kawo mana sunayen muhimman mutanen da za a karrama da kuma dalilin da ya sanya aka zaBe su?
A wajen wannan taron za a bayar da kyaututtukan yabo ga wasu mutane guda huxu da suka wallafa littattafai masu ma’ana, waxanda kuma suka yi tasiri ga ci gaban Adabin Hausa. Waxannan mutanen kuwa su ne Farfesa Umaru Balarabe Ahmed na Zariya, wanda za a ba kyautar yabo saboda ayyukansa a fannin wasannin kwaikwayo; akwai kuma Dokta Bukar Usman wanda ya shahara wajen rubuta littattafan hikaya don kaifafa zukatan matasa; sai kuma Malam Ibrahim Sheme wanda ya kawre a fannin rubutun zube na almara da kuma Hajiya Baida’u Gada wacce ta shahara wajen rubuta tatsuniyoyi irin waxanda gidajen rediyo da talabijin suka dukufa wajen karantawa a halin yanzu, matan aure kuma ke matukar sha’awarsu. Akwai kuma wasu mutane guda uku da za a karrama saboda jajircewarsu da kuma matukar kokarin da suka yi wajen samar da littafan da aka wallafa a cikin harshen Hausa. Su ne Dokta Abdallah Uba Adamu saboda kwazonsa wajen bincike kan rubuce-rubuce da littattafan Hausa, musamman ma wajen kago wasu babbaku masu lankwasa waxanda a harhen Hausa ne kaxai ake amfani da su a na’ura mai kwakwalwa, sai kuma Farfesa Ibrahim Malumfashi na Jami’ar Jihar Kaduna (KASU) saboda kwarewarsa a kan dukkan rubuce-rubucen Dokta Abubakar Imam da kuma yin bincike game da su. Akwai kuma Malam Hussain Hayat, tsohon Manajan-Daraktan kamfanin wallafa na NNPC Zariyaa, wand ya bayar da cikakkiyar gudummawa wajen wallafa littattafan Hausa da yawa.
Bayan wannan taron, me kuma zai biyo baya dangane da marigayi Abubakar Imam da ayyukansa?
Bayan wannan taron kuma za a kafa wata gidauniya ta ci gaba da xaukar nauyin bayar da waxannan kyaututtuka a kowace shekara ga marubuta guda huxu da suka yi bajinta a ayyukansu, a waxannan fannoni guda huxu.
Ko akwai wani shiri da kuke da za ku farfaxo da ayyukan rubuce-rubucen Hausa da sunan Abubakar Imam, domin bunkasa Harshen Hausa?
Bayan taron, za a bayar da cikakken bayanin kafa wannan gidauniyar da kuma waxanda za su tallabe ta, da xaukar nauyin bayar da kyaututtukan, kamar yadda Jami’ar NOUN ta Abuja, watau Jami’ar Koyo Daga Gida ta yi a karon farko na gudanar da tsarin. Baicin haka nan kuma akwai wasu labarai guda goma sha uku da na tsamo daga cikin littafin Magana jari Ce, na kuma mayar da su wasannin kwaikwayo, waxanda tare da zuriyar Marigayi Dokta Abubakar Imam muke son mayar da su littafi da kuma faya-fayen bidiyon da za a dinga sayarwa, ana amfani da abin da aka samu wajen tallafar gidauniyar da za a kafa.
Wane kira za ka yi ga gwamnoni da sarakunan Arewa, dangane da Harshen Hausa da yadda za a bunkasa shi a Arewa a hukumance?
Sarakuna dai su ne iyayen al’umma, kuma masu kula da kare al’adu da xabi’unsu daga gurBacewa. Muna sane da irin cikakkiyar gudummawar da suke bayarwa dangane da haka, kuma muna godiya a gare su saboda dagewarsu wajen shiga cikin dukkan al’amuran da suka jiBanci kyawawan al’adun mutanensu da niyyar haBakawa. Ya wajaba ga sarakuna da kuma masu hannu da shuni su dinga tallabar aikace-aikcen mawallafa littattafai da kuma sauran masu inganta al’adu da xabi’un Hausa ta hanyar shirya gasa iri daban-daban da kuma shirya fina-finai masu ma’ana game da rubutattun halaye da xabi’un al’ummar Hausa da za a dinga kai wa wasu kasashe don faxakar da su game da kyawawan al’adun wannan Bangaren kasar.
Ko akwai wani karin bayani da za ka yi dangane da wannan muhimmin biki, wanda ban tambaye ka ba?
E, to, ba shakka ka taBo wurare masu ma’ana a cikin tambayoyinka, domin ka yi la’akari da inda ke yi wa marubuta kaikayi, ka kuma yi masu susar da ta dace. Saura abu guda kawai nake so in fayyace, shi ne bukata ga hukumomi da masu hannu da shuni da su dinga karfafa gwiwowin marubuta Hausa ta hanyar tallafa masu da dukkan abubuwan da za su bukata don fitar da littattafansu, kuma bayan haka nan su taimaka wajen saye don a samu sukunin rubuta wani. Muna godiya ga dukkan waxanda suka taimaka aka kai ga matsayin da ake a yanzu dangane da harkar rubutun Hausa, da fatan za a ci gaba da haka, sauran jama’an da ba su samu sukunin yin haka ba Allah Ya hore masu abin taimakawa, Ya kuma ba su ikon agazawar, amin.