A kokarin da take yi na kakkabe ayyukan ta’addanci a lokacin bukukuwan Sallah, rundunar ’yan sandan Jihar Gombe ta yi nasarar gano wata maboyar wasu bata-gari.
Kwamishinan ’yan sandan jihar Ishola Babatunde Babaita ne ya bayyana hakan a wata takarda da ya aike wa manema Labarai ta hannun jami’in hulda da jama’a na rundunar, ASP Mahid Mu’azu Abubakar, bisa kokarin da suke yi a lokacin shagulgulan Sallah.
- ISWAP ta kai hari wani kauye a Borno
- NDLEA ta kama Tramadol ta N22bn a hannun ‘abokin harkallar’ Abba Kyari
Ya ce bayan gano mafakar bata-gari, sun kuma ci gana da gudanar da sintiri na sirri a wasu sassan jihar domin tabbatar da sun shawo kan duk wata barazanar da za ta kawo wa zaman lafiya cikas a jihar.
Kwamishinan ’yan sandan ya kuma gargadi ’yan siyasa a jihar da cewa su tsaya bisa kan jadawalin Hukumar Zabe ta INEC kan tsare tsaren hukumar a zaben shekarar 2023 su dai na azarbabi wajen wuce Gona da iri na sabawa tsarin.
Rundunar ’yan sandan ta kirayi iyaye da su mayar da hankali wajen kula da duk wasu shige-da-fice na ‘ya’yansu a lokacin bikin na Sallah.
Kazalika, Kwamishinan ya hori al’umma da su kasance masu kula da duk wani motsi ma mutanen da basu yarda da su ba sannan su gaggauta mika rahoton a kan hakan ta wadannan lambobin waya kamar haka; 08150567771 ko 09036435359.