✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Biden ya caccaki Trump kan goyon bayan Rasha a mas’alar NATO

Ina ta aiki ba dare ba rana don ganin an tsagaita buɗe wuta nan take na tsawon makonni shida a Gaza.

Shugaban Amurka, Joe Biden ya caccaki tsohon shugaban kasar Donald Trump kan shawarar da ya bai wa Shugaban Rasha ta kai wa sauran ƙasashen NATO hari idan ba su kashe kuɗi mai yawa kan tsaro ba.

Biden ya yi caccakar ce kai tsaye yayin buɗe jawabinsa na shekara-shekara a wani zama na haɗin gwiwa da Majalisar Wakilai da Dattawa da ake gudanarwa domin ambato halin da ƙasar Amurka ke ciki.

A cewar Shugaba Biden, gwamnati za ta yi ƙoƙarin ta dawo da Amurkawan da Rasha ke tsare da su.

“Za kuma mu yi aiki ba dare ba rana don dawo da Evan da Paul gida, Amurkawan da Rasha ke tsare da su ba bisa ka’ida ba.”

Biden ya bayyana nasarorin da ya samu kan ababen more rayuwa da masana’antu, ya kuma matsa wa Majalisa ta amince da ƙarin taimakon makamai ga Ukraine, da tsauraran ka’idojin shige da fice da rage farashin magunguna.

Ya kuma tunatar da masu kada kuri’a halin da ya gada a lokacin da ya shiga ofis a shekarar 2021 a yayin da ake cikin bala’in annoba da tattalin arziki, yana mai nuni da yadda kasar ta farfaɗo bayan barkewar annobar.

“Jama’a, na gaji tattalin arzikin da ya karye,” a cewar Biden.

“Yanzu tattalin arzikinmu ya zama abin sha’awa ga ƙasashen duniya a baki ɗaya. An sami sabbin ayyuka miliyan goma sha biyar a cikin shekaru uku kawai. Rashin aikin yi ya yi kasa kwarai.”

Biden ya gargadi Isra’ila da cewa ba za ta iya amfani da agaji a matsayin wani “ciniki” ba yayin da ya yi kira da a gaggauta tsagaita bude wuta na wucin gadi da Hamas a mummunar yakin Gaza.

Biden ya ce, “Ga shugabannin Isra’ila, abun da zan faɗi shi ne taimakon jin-ƙai ba zai zama abin la’akari na yin sulhu ba.

“Sai dai dole ne a fifita karewa da ceton rayukan waɗanda ba su ji ba su gani ba,” in ji Biden.

Ya kara da cewa Isra’ila na da hujjar kai wa kungiyar Hamas da ke iko da Zirin Gaza hari saboda harin da ta kai a ranar 7 ga watan Oktoba.

Ya kuma ce kungiyar Hamas za ta iya kawo ƙarshen wannan rikici a yau ta hanyar sako mutanen da ta yi garkuwa da su.

Sai dai ya kira tasirin da Gaza ke ciki a matsayin abin takaici.

“Ina ta aiki ba dare ba rana don ganin an tsagaita buɗe wuta nan take na tsawon makonni shida,” in ji shi.

Yarjejeniyar za ta “dawo da waɗanda aka yi garkuwa da su gida tare da sassauta rikicin jinkai.”

Kazalika, BBC ya ruwaito cewa shugaba Biden ya takarkare wajen kare salon shugabancinsa a jawabinsa na karshe a kan halin da kasar ke ciki, kafin zaben shugaban kasar da za a yi a watan Nuwamba.

Jawabin na tsawon sa’a daya, wanda ‘yan jam’iyyarsa ta Democrat ke yi masa tafi, ya kasance tamkar yaƙin neman zabe na hamayya tsakaninsa da Donald Trump, inda ya rika caccakar tsohon shugaban na Amurka wanda bisa ga dukkan alamu zai kara da shi a zaɓen na bana.

A jawabin na Shugaba Biden ya riƙa koda kansa da kansa game da manufofi da salon shugabancin nasa, wanda ƙarara yana son shawo kan ‘yan jam’iyyarsa da Democrats, da ke dari-dari a kansa cewa a shirye yake ya gwabza da Donald Trump.

Shugaban mai shekara 81 ya riƙa suka ga Trump da ke zaman abokin hamayyarsa na jam’iyyar Republican da nuna cewa mutum ne da ke son shugabantar Amurka cike da buri na ramuwar gayya da nifaƙa, abin da ya ce ba ta yadda za ka shugabanci Amurka da irin wannan nufi.

Tuni dai Trump ya mayar da martani inda ya aika da saƙonni da yawa ga Biden a dandalin sada zumuntarsa.

Trump ya rubuta cewa “yana magana da fushi a fuskarsa, wannan hali irin na mutanen da suka san ba za su yi nasara ba,” in ji Trump.

“Haushi da kuwa ba su taimaka wajen farfaɗo da ƙasarmu ba!”

Haka kuma, bayanai sun ce yawanci martanin da abokan hamayyarsa ‘yan Republicans suka yi ga jawabin ya mayar da hankali ne a kan batun shige da fice, abin da ake gani kamar wani rauni ne a bangaren shugaban kasar.

Da take mayar da martani ‘yar majalisar Dattawa ta Alabama, ‘yar Republicans Katie Britt, ta ce buri ko mafarkin Amurka ya zama abin tsoro a karkashin mulkin Biden.