✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Besiktas ta ba Eneramo Naira miliyan 100 kudin sallama

dan kwallon gaban kungiyar kwallon kafa ta kasa watau Super Eagles Micheal Eneramo da yake wasa a kulob din Besiktas da ke Turkiyya a karshen…

dan kwallon gaban kungiyar kwallon kafa ta kasa watau Super Eagles Micheal Eneramo da yake wasa a kulob din Besiktas da ke Turkiyya a karshen makon jiya ne suka raba gari da kulob din bayan da kulob din ya sallame shi a watanni goma kafin wa’adin kwantaraginsa ya kare.
Kafar sadarwar Allnigriasoccer.com ta kalato cewa kulob din ya yi hannun riga da dan kwallon ne saboda rashin nuna kwazo.
Rahoton ya ce dan kwallon mai shekara 29 kulob din zai biya shi Yuro dubu 500 kwatankwacin Naira miliyan 100 a matsayin kudin sallamarsa.
Micheal Eneramo wanda ya taba zama kyaftin a kulob din Esperance da ke Tunisiyya yanzu haka ya sake canza sheka zuwa wani kulob din a Turkiyya mai suna Basaksehirspor kuma an ruwaito zai rika karbar albashin Yuro dubu 500 kwatankwacin Naira miliyan 100 a kowace shekara.