✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Benzema ya yi ritaya daga buga wa Faransa kwallo

Benzema ya sanar da jingine takalmansa.

Dan wasan gaban Faransa da Real Madrid, Karim Benzema, ya jingine buga wa Faransa kwallo.

Dan wasan ya bayyana haka ne kwana daya da Faransa ta yi rashin nasara a hannun Ajentina a bugun fanareti a Gasar Cin Kofin Duniya.

Benzema ya wallafa a Twitter cewa, “Na yi iya kokarina kuma na yi kura-kurai wanda hakan ya kawo ni matakin da nake a yau.”

Tun da farko dai Benzema ya samu rauni a kafarsa, wanda hakan ya sa Faransa ta tura shi gida, lamarin da ya janyo ce-ce-ku-ce a tsakanin tawagar ’yan wasan kasar.

Dan wasan na Real Madrid da ya lashe kambun Gwarzon Dan Wasan Duniya na Ballon D’Or, wanda kuma ya cika shekara 35 a duniya a ranar Litinin, ya ce ya yanke hukuncin ne bayan shawara da ya yi.

“Na kafa tarihina a rayuwar kwallo,” in ji Benzema.