Jirgin sojojin saman Najeriya ya sake kai mummunan hari da safiyar Litinin kan maboyar rikakken dan bindigar nan, Bello Turji, a jihar Zamfara.
Aminiya ta rawaito yadda Bello Turjin ya tsallake rijiya da baya yayin wani harin da sojojin suka kai masa a gidansa ranar Asabar.
- Kamanceceniyar Masarautun Kano Da Ingila
- Abin da na fada wa Ummita mako daya kafin a kashe ta – Sheikh Daurawa
Wata majiya daga yankin ta shaida wa Aminiya cewa jirgin yakin ya sake dawowa da safiyar ta Litinin, inda ya jefa bama-bamai akalla guda biyu, da wajen misalin karfe 9:00 na safe.
A wani labarin kuma, wasu ’yan bindiga da ake zargin yaran Turjin ne sun kaddamar da hari kan matafiya a kan hanyar Sakkwato zuwa Gusau, a daidai garin Shinkafi na jihar Zamfara da safiyar Litinin.
Wani mazaunin yankin na Shinkafi, Murtala Wadatau, ya ce maharan sun tare hanyar ne a daidai garuruwan Kwanar Badarawa da Birnin Yero.