✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Beguwa: Dabbar da ke shiga gidajen mutane neman gishiri

Mata kan yi amfani da kayar beguwa a matsayin masillar tsifa, saboda tsayi da kuma girman kayar

Beguwa daya ce daga dabbobin daji, wadda ke da zaro-zaron kaya a sassan jikinta.

Beguwa na da sifa irin ta bushiya, sai dai ta dara bushiya girma, haka ma kayar bayanta ta fi ta bushiya girma da tsayi.

A wasu lokuta, matan karkara kan yi amfani da kayar beguwa a matsayin masilla wajen tsefe suma yayin kitso, saboda tsayi da kuma girman kayar.

Duk da cewa dabbar daji ce, amma akan gan ta jefi-jefi a cikin gari a wurare na musamman, kamar gidajen ajiyar dabbobi da wurin masu tallar maganin gargajiya da mafarauta da sauransu.

Tsarin jikinta

Masana sun ce tsayin beguwa kan kai inci 25 zuwa 36, amma ban da bindinta, domin shi bindin kadai tsayinsa ya kai santimita 20 zuwa 25, ya yin da rikakkiyar beguwa nauyinta kan kai sama da kilogram 20.

Kayar bayanta na mazaunin bangare ne na gashin jikinta kuma garkuwa ce daga farmakin manyan dabbobi.

Kayar a kwance take lib, takan mikar da su ne duk lokacin da ta tsinci kanta a yanayi mara kyau don kare kanta.

Tsayin kayar beguwa kan kai kai inci 3, kaurinta kuma inci 0.079.

Idanuwanta kanana ne, haka ma kunnuwanta, sannan gajerun kafafuwa gare ta, kuma tana da yatsu biyar-biyar da farata masu kwarin gaske.

Kwararru sun ce, dabbar ba ta cika gani sosai ba, sai dai hancinta na da karfin jin kamshi ko wari daga kusa da nesa.

Kazalika, sun ce cikinta na cike yake da kwayan halittun da kan taimka mata wajen narkar da duk abin da ta ci.

Game da yanayin abincinta kuwa, bayan ciyawa da ganyayyaki, hatta kashi ba ta kyalewa idan ta samu, saboda dandanon gishirin da take samu a cikinsa.

Yanayin rayuwar beguwa

Saboda son dandanon gishiri da take da shi, dabbar da ke zaune kusa da gari kan lallaba cikin dare ta shiga gidajen mutane don neman gishirin lasa.

Dabba ce mai sha’awar zama a kurmi, ko wuri mai damshi-damshi da ciyawa sosai, ko a tsauni cikin duwatsu, wasunsu ma har saman bishiya sukan hau.

Kafin haihuwa, takan yi rainon ciki na tsawon kwana 112 (Kimanin wata uku), kuma takan haifi ’ya’ya daga daya zuwa hudu a kan shekar da suka tsara ita da maigidanta.

’Ya’yan kan bar shekar bayan mako daya da haihuwarsu, sannan a tsakanin mako biyu zuwa uku da haihuwa su fara cin abinci mai karfi. A wannan lokaci, uban ne ke dawainiyar kula da yaran.

Suna balaga ne idan sun kai shekara daya zuwa biyu da haihuwa.

Dabbar takan rayu na tsawon shekara biyar zuwa bakwai idan a daji ne, amma takan rayu har tsawon shekara 21 idan a killace take a wuri na musamman.

Shin baya ga sunan ‘Beguwa’, ko mai karatu ya san wannan dabar da wani suna daban a Hausa?