✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Bayanan sahihancin takardun Tinubu sun yi karo da juna —Kotun Koli

Kotun Koli ta bayyana cewa wasikar da ta samu kan takaddamar sahihancin takardun shaidar karatun Shugaba Bola Tinubu daga Jami'ar Jihar Chicago (CSU) da ke…

Kotun Koli ta bayyana cewa wasikar da ta samu kan takaddamar sahihancin takardun shaidar karatun Shugaba Bola Tinubu daga Jami’ar Jihar Chicago (CSU) da ke kasar Amurka sun yi karo da juna.

Shugaban Kwamitin Alkalan Kotun Koli da ke sauran karar da dan takarar shugaban kasa na Jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar ya daukaka, Mai Shari’a John Okoro, ya ce wajibin ne bangaren da ke zargin an aikata babban laifi ya gabatar da gamsassun hujjoji domin tabbatar da zargin da suke yi.

Mai Shari’a John Okoro ya ci gaba da cewa, “Amma abin da gabanmu shi ne wasiku biyu masu karo da juna daga CSU — daya na tabbatar da sahihancin takardun shaidar karatun Shugaban Kasa, dayan kuma na karyatawa. Shin a cikinsu da wanne za a dogara?”

Ya yi wannan jawabin ne a yayin da yake jagorantar zaman kotun a ranar Litinin, wanda bayan nan lauyan Atiku Chris Uche (SAN) ya bukaci kotun ta karbi sabbin hujjojinsu amma lauyan Tinubu, Olujimi Olanipekun (SAN) ya katse masa hanzari da cewa babu dalilin kotun za ta karbi sabbin hujjojin.

Olujimi ya bayyana cewa bukatun bangaren Atiku a karar da suka daukaka na karo da juna, inda a hannu guda yake neman a soke takara Tinubu, a daya hannun kuma yake namen a gudanar da zabe zagaye na biyu a tsakaninsu.

Don haka Olanipekun (SAN) da takwarorinsa na hukumar zabe (INEC) da jam’iyyar APC, sun kuma bukaci kotu ta yi watsi da daukaka karar da da hujjojin saboda ba su da tushe balle makama.

Bayan sauraron bangarorin biyu, kotun ta tafi hutun rabin lokaci.