✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Bayan zargin yi wa takararsa zagon kasa, Tinubu ya ziyarci Buhari a Daura

Ana ganin ziyarar na da alaka da kalaman Tinubu a kan gwamnatin Buhari

’Yan kwanaki bayan ya zargi Gwamnatin Tarayya da kokarin yi wa takararsa kafar ungulu, ta hanyar wasu manufofinta, dan takarar Shugaban Kasa na jam’iyyar APC, Bola Tinubu, ya ziyarci Shugaban Kasa Muhammadu Buhari a mahaifarsa da ke Daura a Jihar Katsina.

Tinubu dai ya sami rakiyar Gwamnan Jihar ta Katsina, Aminu Bello Masari da wasu Gwamnonin APC, yayin ziyarar da daren Juma’a, kamar yadda wasu majiyoyi suka tabbatar wa Aminiya.

Sai dai babu cikakkun bayanai kan ainihin makasudin ziyarar ta Tinubu zuwa Daura.

A ranar Alhamis ce Aminiya ta rawaito yadda Tinubu ya yi zargin gwamnati mai ci ta kirkiro matsalar wahalar man fetur da canjin kudin da suka jefa ’yan Najeriya cikin kunci a ’yan kwanakin nan da gangan ne domin ta gurgunta takararsa.

Lamarin dai ya yi ta yamutsa hazo a fagen siyasar Najeriya, inda wasu suke zargin akwai alamun baraka tsakanin dan takarar da gwamnatin jam’iyyarsa.

Amma Kakakin Kwamitin Yakin Neman Zaben Tinubu, Byo Onanuga, ya zargi ’yan adawa da kokarin rura wutar, inda ya ce suna kokarin haddasa fitina ne kawai ta hanyar juya masa magana.

Kazalika, ita ma Fadar Shugaban Kasa ta ki ta ce uffan a kan batun, kodayake akwai rade-radin cewa ziyarar ta Tinubu na da alaka da kalaman nasa.

A cewar wata majiya da ta nemi a sakaya sunanta, “Tinubu ya gana da Gwamna Aminu Bello Masari na Katsina da Babagana Umara Zulum na Borno da kuma na Kebbi, Atiku Bagudu, kafin su rankaya su tafi Daura wajen Buhari, kodayake Zulum bai bi su ba.

“Watakila Tinubun ya fuskanci duk inda suka je kamfe suna fuskantar matsala daga mutane, shi ya sa ya ga ya dace ya tattauna da Shugaban a kan lamarin,” in ji majiyar.

%d bloggers like this: