Adam Namadi, dan tsohon Mataimakin Shugaban Najeriya, Namadi Sambo, ya nemi wakilan zabe wato daligets su dawo masa da kudin da ya ba su bayan rasa tikitin takara.
Wannan na zuwa ne yayin da zaben fid da gwanayen takara na jam’iyyar PDP ke ci gaba da gudana a fadin kasar.
Aminiya ta ruwaito cewa Adam ya sha mugun kaye ne bayan samun kuri’u biyu kacal zaben fid da gwanin takara na dan majalisa mai wakiltar mazabar Kaduna ta Arewa a Tarayya.
Gabanin hakan dai Adam ya bai wa wakilan zaben Naira miliyan biyu-biyu da zummar su kada masa kuri’ar tsayar da shi a matsayin dan takarar kujerar Majalisar Wakilai naazabar Kaduna ta Arewa.
Haka kuma, dan tsohon Mataimakin Shugaban Kasar ya yi alkawarin kara wa wakilan zaben Naira miliyan daya da rabi-rabi domin samun nasara, amma shi ne ya tashi da kuri’u marasa yawa duk cikin manema takarar kujerar.
Tuni dai su kuwa wakilan zaben suka cika lalitarsu da miliyoyin naira daga aljihun manema takarar da suka fito kwansu da kwarta da zumudin ganin sun yi galaba a kan abokan karawarsu.
A karshe dai Sama’ila Suleiman, dan majalisar Kaduna ta Arewa mai ci a yanzu shi ne ya sake lashe zaben, inda ya tika Adam Namadi da kuma Shehu Usman ABG da kasa.
Sama’ila Suleiman wanda a kwanan nan ya sauya sheka daga jam’iyyar APC zuwa PDP, ya samu kuri’un wakilan zabe 22 yayin da Shehu Usman ABG ya samu 14.
Wakilan zaben sun shaida wa Aminiya cewa Sama’ila Suleiman ya rarraba musu kudi daga kan naira miliyan 3.5 zuwa miliyan 4, yayin da shi kuwa ABG ya danka musu Naira miliyan 2.5, inda Adam Namadi ya rarraba musu naira miliyan biyu kacal.
Sai dai bayan shan kasa, ABG da Adam Namadi sun bukaci wakilan zaben su gaggauta dawo musu da kudadensu.