Bayan shafe kwana 45 a hannun ’yan bindiga, basaraken nan na Jihar Neja, Dodo na Wawa, Dokta Mahmoud Ahmed Aliyu ya shaki iskar ’yanci.
Rahotanni sun tabbatar da cewa ya isa gida ne da misalin karfe 7:30 na daren Talata bayan an biya Naira miliyan 10 a matsayin kudin fansarsa.
- Daga Laraba: Neman mafita daga matsalar watsi da tarbiyyar ’ya’ya (2)
- Za a kashe N863bn don yakar talauci — Gwamnatin Najeriya
Wazirin Wawa, Alhaji Ja’afar Ibrahim Bio ne ya tabbatar da kubutar basaraken ga wakilin Aminiya ta wayar tarho, ko da yake ya ki cewa uffan akan nawa aka biya a matsayin kudin fansa.
Ya ce, “Mun samu mun kubutar da shi, yanzu haka yana gida. Nima yanzu ina fadar.
“Ina tabbatar maka a matsayina na Waziri cewa mun kubutar da Dodo. Ya dawo gida wasu ’yan mintuna kafin karfe 8:00 na daren Talata kuma yana cikin koshin lafiya.
“Amma kan batun nawa aka biya kudin fansarsa, wannan ba zan iya fada maka ba, abu mafi muhimmanci dai shi ne an kubutar da shi.”
A wani faifan bidiyo da iyalansa suka tura wa Aminiya, an ga basaraken da farin rawani iyalansa na yi masa maraba a cikin fada lokacin da ya dawo.
A dai sace Dokta Mahmud ne bayan wasu ’yan bindiga dauke da muggan makamai suka kutsa kai fadarsa da wajen misalin karfe 9:00 na daren ranar hudu ga watan Satumban 2021 zuwa wani wajen da ba a san ko ina ne ba.
Ya kubuta ne bayan an shafe tsawon lokaci ana cinikin kudin fansarsa, wanda da farko suka bukaci a biya su Naira miliyan 25.