Gwamnatin jihar Kogi ta kaddamar shirin yi wa ’yan jiharta allurar rigakafin cutar COVID-19, duk kuwa da karayata samuwarta a baya.
A watan Janairun da ya gabata dai an ga Gwamna Yahaya Bello a cikin wani faifan bidiyo da ya karade gari yana shawartar mutane da kada su kuskura su karbi rigakafin, inda ya ce ana son yin amfani da ita ne wajen kawo wata cutar da za ta kashe mutane.
- Har yanzu ba mu san adadin daliban da aka sace a Jami’ar Greenfield ba – Gwamnatin Kaduna
- Majalisar Dattawa ta amincewa gwamnati ciyo bashin $1.5bn da €995
To sai dai a wani mataki mai kama da mi’ara koma baya, Gwamnatin jihar a ranar Laraba ta kaddamar da shirin yi wa ’yan jihar rigakafin.
Duk da haka, gwamnatin ta ce ba za ta tilasta wa kowa karbar rigakafin ba, kuma ba za ta hana dukkan mai son a yi mishi ita ya samu ba.
Kwamishinan Lafiya na jihar, Dakta Haruna Saka yayin kaddamar da shirin a Lakwaja ya ce jihar ta karbi alluar AstraZeneca kusan guda 16,900, yayin da suke sa ran samun wasu nan ba da jimawa ba.
Ya kuma jinjinawa Gwamna Yahaya Bello kan abinda ya kira da irin namijin kokarin da yake yi wajen kare lafiyar al’ummar jihar, ya kuma gode masa saboda kawo rigakafin jihar da ya yi.
Sauran muhimman abubuwan da suka wakana yayin bikin kaddamarwar sun hada da yin allurar ga manyan mukarraban Gwamnatin Jihar, ciki har da shugaban Hukumar Kula da Lafiya a Matakin Farko ta Jihar, Dakta Abubakar Yakubu.
Aminiya ta lura cewa ayarin jami’an lafiyar da zasu yi wa jama’a rigakafin sun zo da yawa amma mutane ba su fito yadda ya kamata ba.
Rahotanni sun nuna cewa rashin fitowar mutanen ba zai rasa nasaba da imanin da suka yi cewa allurar ta Kabul ce kuma wadanda aka yi wa na iya mutuwa cikin kankanin lokaci.