Masallacin Annabi (SAW), Madina
Fassarar Salihu Makera
Hamdala da taslimi.
Ya ku Musulmi! Wane Alhaji ne bayan ya dawo daga Hajjinsa zai rika zuwa wurin bokaye da masu sihiri, ya rika gaskata ma’abuta bugun kasa da masana taurari da masu duba ko ya rika neman tabarruki da itattuwa yana shafa duwatsu ko ya daura layu da guraye? Wane Alhaji ne bayan ya dawo zai rika wasa da Sallah ko ya hana Zakka ko ya ci riba da rasahawa ya rika tu’ammali da kwayoyi da giya da sauran kayan maye. Ko ya rika yanke zumuna ya auka wa manyan kaba’irai da sauran zunubai?
Ya mahajjatan Dakin Allah! Ya wadanda suka hanu daga abubuwan da shiga Harami ya haramta a lokacin aikin Hajjin Dakin Allah Mai alfarma! Akwai wasu abubuwa da aka haramta da’iman a tsawon rayuwa, don haka ku guji aikata su ko kusantansu. Allah Madaukaki Yana cewa: “Wadancan iyakokin Allah ne, saboda haka kada ku ketare su. Kuma wanda ya ketare iyakokin Allah, to wadannan su ne azzalumai.” (K:2:229).
Ya ku Musulmi! Wanda ya yi talbiyya ga Allah, yana mai amsa kiranSa, yaya zai amsa wata da’awa ko akida ko mazhaba ko kiran da ke warware addinin Allah, wanda ba a karbar wani addini daga wani mutum koma bayansa? Wanda ya yi talbiyya a Hajji yaya zai yi hukunci bayan haka da water shari’ar Allah, ko ya mika wuya ga wani hukunci sabanin nasa ko ya yarda da wani sako bayan naSa? Duk wanda ya yi talbiyya a Hajji, to ya ci gaba da wannan talbiyya a kowane wuri da zamani ta amsa umarnin Allah ta duk inda ya juya fuskarsa da inda ya samu kansa kada ya yi kai-kawo kan haka kada ya raurawa. A’a ya yi hakan cikin kankan da kai da tawali’u da ji da da’a.
Ya bayin Allah! Ya wanda rana a wadannan ranaku ta fadi yana aikata sabo da zunubai! Ya wanda ayyukan alheri da rahama suka kubuce masa yana shagalalle da wasanni da ayyukan ki! Shin ba za ka yi dubi zuwa ga ayarin Alhazai da masu Umara da masu ibada ba? Shin ko ba ka ji saututtukan masu talbiyya da kabbarori da hailala ba ne?
Ya wanda ya wayi gari cikin sabo kuma ya yi yammaci a cikinsa, yana cewa zan tuba yau ko gobe! Ya wanda zuciyarsa ta wayi gari a cikin bata ko ke rayuwa cikin jahilci, sha’awoyi suka dabaibaye shi, ka tuna daren da za ka kwana a kabari kai daya. Ka gaggauta tuba tun kafin dama ta kubuce maka, ka riski abin da ka rasa kafin a ce maka me ka gabatar? Ka ciru daga aikata zunubi da laifuffuka. Kuma ka sani lallai Allah Yana shimfida hannunSa da rana domin mai laifin dare ya tuba, kuma Yana shimfida hannunSa da dare domin mai laifin rana ya tuba.
Ya kai wanda ya juya ga aikata nau’o’in ibada! Ka lizimci tafarkin daidaituwa, ka dawwama a kan aikin, domin duniya ba gidan zama ba ne. Ka guji lalaci da riya, domin da yawa karamin aiki niyya kan girmama shi, kuma da yawa babban aiki niyya kan maida shi karami. Wani magabacin kwarai ya ce: “Wanda ke son ya yi farin cikin kammaluwar aikinsa, to, ya kyautata niyyarsa.” Ka zama mai tsoro da saunar yiwuwar rashin karbar aikinka. An karbo daga A’isha (RA) ta ce: “Na tambayi Manzon Allah (SAW) kan wannan aya: “Wadanda suke bada abin da aka ba su alhali zukatansu suna cikin tsoro.” (Al-Mumin: 60). Sai na ce: Shin suna shan giya suna sata ne? Sai Manzon Allah (SAW) ya ce: “A’a, ya ’Yar Siddik. Su suna azumi suna Sallah, suna sadaka, sai dai suna tsoron ko ba za a karbi ayyukansu ba ne. “Wadannan su ne suke gaggawa a cikin alherori, kuma suke rigegeniya kansu.” (Al-Mumin: 61)” Tirmizi ya ruwaito shi.
Don haka ku bi Allah ta takawa ya ku muminai a kowane lokaci, ku tuna fadin Allah a cikin Littafi Mabayyani. “Iyaka Allah Yana karba ne daga masu takawa.” (Ma’ida:27).
Allah Ya albarkace ni da ku a cikin bin Alkur’ani da Sunnah, kuma Ya amfanar da ji da ku da abin da ke cikinsu na ayoyi da hikima. Ina fadin abin da kuke ji, ina mai neman gafarar Allah gare ni da ku da sauran Musulmi daga dukkan zunubi da kuskure. Ku nemi gafararSa, lallai ne Shi Mai gafara ne Mai jin kai.