Gwamnatin Tarayya ta fara yunkurin karkata akalar ciyo bashinta zuwa kasashen Turai bayan ta fuskanci jan kafa daga kasar China.
Rahotanni sun ambato Ministan Sufuri, Rotimi Amaechi na cewa Najeriya na shan wahala matuka wajen karbo bashin daga China.
- Bom ya kashe Jagoran Civilian JTF, 5 sun jikkata a Borno
- Najeriya A Yau: Ma’anar hijabi a idon duniya
Ministan ya tabbatar wa manema labarai a Fadar Shugaban Kasa bayan kammala taron Majalisar Zartarwa na ranar Laraba cewa, “Muna ta zaman jiran China ta ba mu bashin da muka roka, amma har yanzu sun ki bayarwa. Sai ja mana rai kawai suke yi.
“Haka za mu ci gaba da zama ke nan har karshen wa’adin mulkinmu? Amsar ita ce a’a, saboda tuni muka garzaya bankin Standard Chartered, kuma sun amince za su ba mu wani bangare na kudaden.
“Da bashin muke kokarin yin aikin titin jirgin kasa na Fatakwal zuwa Maiduguri. Shi kuma na Kano zuwa Legas, wani bangaren kudadensa za su fito daga bankin, wasu kuma za su fito daga bankunan kasuwanci na China,” inji Amaechi.
Sai dai da aka tambaye shi adadin kudaden da za a ciyo bashi daga kasashen Turai din, Ministan ya ce ba shi da alkaluman a ka, dole sai ya koma ofis.
Binciken Aminiya ya gano cewa yanzu haka akwai ayyukan gwamnati da dama da kasar ta China ce ke samar da kudaden yin su.
Shi ma a nasa bangaren, Ministan Ayyuka da Gidaje, Babatunde Fashola, ya ce Majalisar Zartarwar ta kuma amince da ware Naira biliyan 115 don aikin mayar da hanyar Kano zuwa Kazaure zuwa Kongolom a Jihar Katsina ta zama mai hannu biyu.